Get New DJ Mixes
Kannywood

Dawowar Rahama Sadau Kannywood Alkairee Ne Inji – Lawan Ahmed

Jarumi Lawan Ahmed ya fito fili ya nunawa duniya matsayarsa akan dawowar jaruma Rahma Sadau cikin kannywood, bayan kungiyar Moppan tayiwa jarumar korar kare. a zantawar da ya yi da Mujalla Fim yace dawo da Rahma Sadau shi yafi alkairi.

 

Acewarsa: Tun farko hukuncin da yankewa jarumar ya yi tsauri da yawa. ba hukuncin kura ya kamata ba. domin ba’a taba kama Rahma Sadau ta aikata laifi makamancin haka ba. bisa la’akari da wannan sai akira ta ayi mata kashedi da jan kunne. amma kawai sai akace an kore ta gaba daya.

 

Amadadin ta daina fim. sai kuma likafa taci gaba da koma America dan cigaba da sana’ar fim din ta. kun ga kenan, anyi- ba- ayi ba kenan. dawo da ita kasa Nageria da akayi shine mafi alkairi. domin ko ba komai asami haraji da ita (Rahma Sadau). Amma idan da tana America Harajin na kasar America zata bayar.

 

Sannan duk uba nagari baya korar dan sa daga gida, dan ya aikata ma shi laifi. nasiha ita ke biyar da yaro ko yarinya.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.