-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Dausayin Masoya: Ashe Gara Tamaidani Bansani ba!


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Dausayin Masoya

Ashe Gara Tamaidani Bansani ba!

Daga Sabiu Danmudi Alkakanawi

Mai Karatu Barkanka da warhaka, da fatan kana cikin koshin lafiya, Allah yasa haka amin.

Labarin namu nayau ya fito ne daga wajen wani bawan Allah mai suna Abdul, inda yafara da cewa “Amira dai budurwata ce, wadda muka shafe kusan shekaru biyu muna soyayya. Tana nunamin soyayya matuka, haka nima ina matukar kaunarta.

Hakan yasa ni da ita muka zama daya, kusan duk wasu sirrikana da al’amurana ta sani, sannan kuma nakanyi kokari wajen magance mata duk wasu matsaloli da suka kunno mata kai, musamman ma na kudi. Kamar ankon biki, siya mata kayan kwalliya, siya mata waya da sa mata katin waya, da sauransu.

Muna tsaka da soyayya kwatsam sai rannan takirani a waya, dagawata ke da wuya naji ta fashe da kuka, hankalina a tashe yake a lokacin saboda naji kukan nata yayi yawa, amma haka dai nayi ta maza nafara rarrashinta gami da tambayarta me yafaru? Dakyar dai nasamu ta sassauta kukan.

Cikin shasshekar kuka tacemin wai iyayenta ne zasu yimata auren dole, kuma sun kammala duk wasu shirye-shirye na bikin, abin da yarage kawai jira ake nan da sati biyu a daura aure.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 3

- Advertisement -

Tun da naji wannan magana daga bakinta gaba daya jikina yafara rawa, gashi lokacin a tsaye nake, ji nake kamar zan fadi kasa. Wayar tawa ma subucewa tayi tafadi kasa.

Haka dai nadaure nayita bawa zuciyata hakuri, nacigaba da addu’a har Allah yasamin hakuri da dangana.

Bayan anyi bikin Amira da ‘yan kwanaki, sai muka hadu da wata kawarta a hanya, bayan mun gaisa sai tacemin dama ko inason ganinka, saboda zamuyi wata magana mai muhimmanci.

Da muka sami waje a gefe muka kebe, tacemin Abdul magana ta gaskiya dama can Amira bata sonka, tayi soyayya dakaine kawai dan biyan bukatar kanka ba wai dan tana sonka ba. Lokacin da takiraka a waya tace maka za ayi mata auren dole muna wajen, kuma duk kukan da kaji tayi na karya ne.

Tacemin kayi tunani sosai, sau nawa kana cewa Amira zaka turo magabatanka tana cewa ba yanzu ba, ko kuma tayima hanya-hanya? Da tafadamin haka sai nashiga kogin tunani, sai nagano gaskiyar abin da tafadamin.

Saboda duk lokacin da nayiwa Amira maganar turo magabatana sai naga ta bata rai, idan kuma namatsa mata sai tacemin nabari sai ankwana biyu, kwana biyun da ban gansu ba kenan.

Daga nan mukayi sallama da kawar Amira. Dan haka nayanke shawarar turo da labarina cikin wannan shiri mai albarka, domin jama’a subani shawara, don kada in sake fadawa wani tarkon.” Wannan shine labarin Abdul.

Kaima zaka iya turo da labarinka ta wadannan hanyoyin.
Whatsapp: 08148337698
Email: [email protected]
Sai munji daga gareku.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: