Daukar Nauyin Karatun ‘Ya’yan Talakawa Adam A. Zango Dan Damfara Ne

1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Binciken Auwal Mustapha Imam

Zaku iya lura na cire labarin da na wallafa na cewa Adam A Zango ya dauki nauyin karatun ‘ya’yan talakawa 101 domin yin karatu a makarantar “Farfesa Ango Abdullahi a Zariya. Daga baya na yi bincike akan batun inda na gano zuki-ta-malle ce kawai.

Akwai makaranta mai sunan Ango Abdullahi wacce bada jimawa ba ta sauya sunanta, wacce Adam Zango ya sanya ‘ya’yansa amma daga baya ya cire su. Akwai hoton Zango da Malaman makarantar da kuma Ango Abdullahi wanda suke amfani da shi wajen tallata makarantar, kuma Ango Abdullahi ya sha jan kunnensu wajen daina amfani da shi ana damfara.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 6

Makarantar ta kitsa wannan damfara ne don tallata kansu a duniya, kuma a halin yanzu mutane na ta tururuwar zuwa don tabbatar da gaskiyar labarin.

A karshe ina ba da hakurin wallafa wannan labarin karya, kana kuma ina kira ga gidajen yada labarai irin su Daily Trust su garzaya Makarantar don tantance gaskiyar wannan batu.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: