Shararriyar ‘yar wasan kwaikwayon nan Saratu Gidado da aka fi sani da Daso,ta bayyana nadamar ta tare da tuba ga masarautar Kano bisa rike tagwayen masu da tayi a cikin wani fim da ake daukar sa mai suna ‘Dan Tijara’A cikin wannan fim dan wasan kwaikwayo Ali Nuhu ne ya fito a matsayin Sarki kuma bayan kayan sarauta irinsu rawani da alkyabba da malafa da ya saka,har ma ya rike tagwayen masu.To amma daga bisani wasu daga cikin ‘yan wasan musamman Mata irinsu Halima Atete da mai gado da ita kanta Saratu Daso sun dauki tagwayen masu sun yi hoto dashi lamarin da ya zame wa ita Daso dan zani.A cewar Daso ta dauki hoton da masun ne saboda sha’awa da kuma ganin cewar ba na ainihi bane,amma sai gashi abin bai yiwa masarauta dadi ba,dan haka Daso ke neman afuwar mai martaba Sarki dama duk ahalin masarautar bisa wannan laifi da aka ce tayi.Wata majiya daga cikin gidan sarkin Kano ta bayyana cewar rike tagwayen masu a wurin mace ya sa6a da dokokin masarautar Kano,domin sarkin Kano ne kadai aka amince ya rike shi.Wannan majiya tace a baya akwai zamanin da wani Sarkin a Jihar Jigawa ya taba kokarin yin tagwayen masu amma daga masarautar Kano aka tilasta masa ajiyewa.Tagwayen masu dai wasu masu ne guda biyu masu launin kore da ja,da sarakunan Kano tun kafin zuwan fulani suke rikewa.Kuma ya dauko asali zamanin wasu sarakunan Kano tagwaye da suka yi mulkin Kano a lokaci guda.Daso wacce itace jakadiyar sarkin Kano zamanin yana Dan majen Kano,ta ce batasan cewar rike tagwayen masun laifi ne a gare ta ba dan haka take jaddada tuba ga fadar Kano.sai dai kuma ko fada zata ja kunnen sauran matan da suma suka dauki hoto irin na Daso ?
Ga hotunan kamar haka
Source Nasiru Salisu Zango
Add Comment