Mu Kyakyata

Dariya Zalla – Wayayyen Dan-Fulani A Banki

Wani dan Fulani ne maman sa ta aike shi Banki domin ya sakawa yayansa kudin makaranta, koda ya isa harabar bankin sai ya ga mutane akan layi suna ta mika wata takarda ana ba su kudi.
Bai yi kasa a gwiwa ba sai ya tambayi wani malami akan cewa yana son ya tura ma yayansa kudi ne amma bai san yadda ake yi ba, sai mutumin ya karbi kudin yace je ka dauko tela a nuna ma ka yadda ake yi, sai ya ce ma mutumin ya gode.

Kawai sai ya fito daga bankin ya hau babur na shi bai yi burki ko ina ba sai shagon telan unguwar su ya ce ma shi don Allah ya zo suje banki zai dan yi ma shi wani aiki ne.
Telan kuwa da jin hakan kuwa ya dauko tape din sa su ka koma bankin, da isar su sa ga mutumin nan yana ta fada kai dan-fulani daga ka miko tela sai kaje kayi zaman ka sai dan-fulanin yace ai ga telan tare da ni kasan unguwar mu da dan tazara ai sai kowa a harabar bankin su ka kwashe da Dariya!

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.