Mu Kyakyata

Dariya Zalla: Mune Ba Ta Buya

Wata mata ta shiga taxi za ta unguwa sai ta zauna gidan gaba a mota, ana cikin tafiya sai direban ya juyo ya kalleta da ita da danta sai yayi dariya yace “gaskiya hajiya ban taba ganin munmunar irin danki ba” sai ta dube shi tayi tsaki “mtseww” sannan tace ya tsaya ta koma baya.
Ta koma baya ta na ta zage-zage sai wani tsoho dake bayan matar yake “tambayarta me yafaru?” sai ta fada masa abinda direban yace mata sai tsohon yace “kin mare shi?” sai tace “A’a” sai yace “kawo birin da ke hannun ki in rike maki ki je ki mareshi”
Toh a cikin su wa yafi mata rashin mutunci?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: