Mu Kyakyata

Dariya Zalla: Idan Ina Yi; Ina So Na Ga Kowa Ma Na Yi

Wani shakiyin Bazazzagi ne ya yi dinkinsa babbar riga mai asake akan wata dalleliyar shadda ruwan kwai. Da ka ganshi ka ga mai hannu da shuni. Ai kuwa sai ya nufi gidan abinci (Restaurant), ya samu waje ya zauna ya kwalawa mai restaurant kira da karfi ya ce “Hado min plate na Naira 2,000 kuma ki hadawa kowa da ke wajen nan plate na Naira 3, 000 saboda idan ina cin abinci, ina so naga kowa yana ci”.
Duk mutanen da ke wajen suka fara godiya yayin da mai restaurant ta zubawa kowa nasa ta kawo masa hadin girma. Shinkafa da dankalin turawa da farfesun kayan ciki ko kifi ko naman kai, ya dai danganta da abinda mutum ke so. Kana ga hadin kwadon kayan lambu da a turance a ke kira da salad
Bayan mutumin ya gama cin abinci sai ya kuma cewa mai abincin “kawo min abin sha na Naira 500 kuma ki baiwa kowa na Naira 1, 000 saboda idan ina shan abu, ina so naga kowa yana sha”.
Mai Restaurant ta kaiwa kowa kayan shaye-shaye kala-kala. Nan fa mutanen wajen suka barke da shewar “Allah ya kiyaye ka!”
Bayan mutumin ya gama sai ya cewa mai Restaurant “kawo min resit na biya kudina kuma ki kaiwa kowa nasa resit ya biya kudinsa, saboda idan ina biyan kudina ina so naga kowa yana biyan nasa”.
Yanzu haka mutumin yana kwance a asibiti saboda dan karen dukan da masu gidan abinci da kuma mutanen da ya saka suka ci abincin da basu yi niyya ba suka yi masa
Yanzu haka ni kuma ina kwance ina dariya, saboda idan ina dariya ina so na ga kowa na dariya

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.