Mu Kyakyata

Dariya Zalla: Baba Wallahi Ko kai Ne Sai Ka fadi Jarrabawar Nan

Ga wata zantawa tsakanin mahaifi da dansa akan fitowar jarrabawar JAMB. Mu sha dariya………
BABA: Na ji ance jarrawabawar Jamb ta fito, me ka samu?
YARO: Baba monitanmu baici ba.
BABA: Assha! Kai fa?
YARO: Ai Amina ma data wakilci makarantarmu a gasar turanci da lissafi kuma ta yi ta daya ita ma ta
fadi jarabawar.
BABA : Subhanallahi! To kai fa?
YARO: Aliyu, mai yi mana na daya a Aji shima baici ba.
BABA : Ikon Allah! To kai kuma fa?
YARO: Musa mai yi mani extra lesson shima baici ba.
BABA : Kai abun bai yi dadi ba! To kai fa?
YARO: Shin wai Baba, Ni Aljani ne? Duk wadannan fa  sun fi ni kokari kuma ga shi duk sun fadi ya za ayi ni inci? Wallahi Baba ko kai ne sai ka fadi…
HaHaHaHaHaHaHa…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: