Labarai

Dangote ya nemi kotun Amurka ta bada umarnin a damke tsohuwar budurwar sa

Fitaccen attajiri kuma ɗan kasuwan da ya fi kowa kudi a Afrika, Aliko Dangote, ya roki kotun Amurka dake sauraren karar da ya shigar akan tsohuwar budurwarsa Autumn Spikes, wacce kwanan nan ta shiga kafafen sada zumunta ta tona asirin soyayyar da suka murza na kusan shekaru 10 da ta bada umarnin a damke ta.

Ya shigar da “takardar neman kotu ta tabbatar da haka, a matsayin hujja na farko da aka mika.”, ta hannun lauyoyinsa da ke Amurka a ranar 25 ga Janairu, kwanaki biyar bayan ya shigar da karar a wato ranar 20 ga Janairu.

” A dalilin haka mai shigar da kara ya roki kotu da ta amince da umarni na farko kuma ta umarci wacce ake kara Autumn Spikes da ta nuna hujjojin da ya zai sa ba za a ba da damar a damke ta ba.,”

Dangote ta hannun lauyoyin sa ya ce bai ga dalilin da zai sa ya rika biyan wata mata can da ba matarsa a baya ba kuma babu alkawarin aure a tsakanin makudan kuɗi haka kawai don ta bata masa suna ba.

Cikakken labarin

Cin fuska da rainin hankali ne tayin $15,000 da Dangote ya yi min – Tsohuwar Budurwar Dangote

Tsohuwar budurwar Aliko Dangote, Autumn Spikes ta bayyana cewa tayin da Attajiri Dangote yayi mata na bata $15 da kuma $2500 duk wata don ta kama bakinta ta yi shiru game da soyayyar da suka yi cin fuska ne da raina mata wayau da yayi.

” Raina min hankali Dangote yayi wai zai bani $15,000 sannan ya rika bani $2,500 duk wata na yarjejeniyar in kama baki na in yi shiru kada in tona soyayyar da muka yi a baya, haba wuce nan.” In ji Spikes

Sai dai kuma bata yi bayanin ko tsawon watanni nawa bane Dangote yayi alkawarin zai rika bata wannan kudi.

” Bayan haka ni Spikes har yanzu ba a ba a kawo mini sammacin karar ba, shi yasa na saka komai a Instagram ku zo mu tattauna.

Yadda tsohuwar budurwata ta kitsa tuggun karbar $ 5,000,000 daga hannu na – Dangote

Shahararren Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya fadawa wata kotun Amurka yadda tsohuwar budurwarsa Ba’amurkiya, wacce ta fallasa wani hoton sa da ita a shafukan sada zumunta, ke kokarin karbar dala miliyan 5 daga hannun sa.

PREMIUM TIMES ta samu takardun karar da aka shigar da sunan karya a kan matar da aka ambata da suna Autumn Spikes a Kotun Yankin Miami-Dade da ke Florida, kasar Amurka.

Attajirin ya yi amfani da sunan da ba a san shi ba, John Doe, da kuma karin inkiya ‘AD’, da ke nufin Aliko Dangote, a matsayin sunan sa.

Yana neman “sama da $30,000” a matsayin diyya akan Ms Spikes.

Daya daga cikin takardun kotu da mai gabatar da kara ya shigar a ranar 22 ga Janairu, mai taken, ‘Korafin koke don karar yanke hukunci kan (game da) neman karbar kudi don neman umarnin sassauci’.

Takardar, cikin sauran wasu, wanda PREMIUM TIMES ta samu, ta zargi Ms Spikes da batanci, yin amfani da yanar gizo da kuma karya yarjejeniya da su ka yi a tsakanin su na yin soyayyar su cikin sirri ba tare da an saka wani abu makamancin haka a shafukan yanar gizo ba.

Bayan haka ta nemi Dangote ya rika biyanta kudade masu, $5000,000 a matsayin kudaden da zata rika kula da a kanta wanda ba bu wani dalilin da zai sa a yi haka.

Irin wannan kudade saurayi yakan bada su ne idan ga budurwarsa idan ba za su yi aure ba amma kuma suna tare domin ta ci gaba da kula da kanta.

Ita Autumn Spikes ta gabatar da bukatar cewa mai shigar da karar ya biya ta dala miliyan biyar ($ 5,000,000.00) kamar yadda yake a Hujja ta 1, “Takardar kotu ta Dangote.

Soyayyar Dangote da Spikes

Ita dai Spikes ta rika sassaka hotunanta da Dangote a shafinta na Instagram, inda wasu daga cike ke nuna shi a kwance cikin bargo amma, duwaiwan sa a waje ya na rike da waya.

Daga baya ta ciccire wasu hotunan. Sai dai tace ta yi haka ne domin gargadin Dangote ya je ya wanke kansa daga wani zargi inda wata budurwarsa Bea Lewis ta saka hotunan su a yanar gizo.

Dangote ya yi ƙoƙari ya rabu da Spikes cikin gaggawa ganin cewa harkar ta baci.

Bayan neman kawo karshen alakar sa da Spike, ya nemi ta amince da wani yarjejeniyar rashin bayyana abinda ya hada su a baya da soyayyar da suka yi har abada ta hanyar azo a zauna a sasanta a kuma rattaba hannu a wata yarjejeniyar sirri.

Daga nan ne fa Spikes ta nemi dala miliyan 5, ta hannun wakilan ta a matsayin soman tabin yarjejeniyar.

Ita wannan bukatar ta biyo bayan imel da lauyan Dangote, Fleisher, ya aika wa lauyan Spikes, Paul Petruzzi, a ranar 13 ga Janairu, inda ya nemi ” Asalin bayanan bukatar Spikes”

Da yake mayar da martani ga sakon imel din Fleisher, Petruzzi ya bayyana alakar da ke tsakanin abokin huldarsa da hamshakin attajirin wato Dangote a matsayin “Dangantaka da har yanzu a na cikinsa sannan dadaddiya ta kusan shekaru goma da suka gabata tun tana Spikes ta na ƴar budurwa.”

Dangote ya ce wannan wata makarkashiya ce kawai aka shirya masa na babu gaira babu dalili. Sannan ya ce dama can ita wannan yarinya wato Spikes ta yi masa barazanar tozarta shi ko kuma ta bashi zabi biyu, ko su ci gaba da murza soyayya ko kuma ya aure ta kawai ko kuma ya dankara mata Daka miliyan 5 ta tsuke bakinta ta yi shiru.

Dangote ya ce ita ce za ta biya shi diyya bayan ta karya alkawarin da suka dauka na yin soyayya a boye cikin sirri ba tare da wani ya yaɗa abin a yanar gizo ko kuma kafafen yaɗa labarai ba.

Haarun

Haruna Lawan Usman is a certified Animal Health and Production Technologist, with more than 4 years experience in Animal Health and Production Technology.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: