Labarai

Dan Shugaba Buhari Zai Auri ‘Yar Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero

Daga Comr Abba Sani Pantami
Yusuf Buhari, dan gidan shugaban kasa Muhammadu, na shirin angwancewa da diyar Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, Zahra Ado Bayero, kamar yadda Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Zahra Bayero yanzu haka na karatun ilmin zanen gine-gine a kasar Birtaniya yayinda shi Yusuf Buhari ya kammala karatunsa a jami’ar Surrey, Guildford, a Birtaniya.

Majiyoyi sun bayyana cewa za’a gudanar da bikin cikin watanni biyu zuwa uku.

“An kaddamar da shirye-shiryen bikin. Kamar yadda al’ada ta tanada, iyayen mijin sun kai gaisuwa wajen iyayen Zahra,” cewar majiyar da aka sakaye sunanta.

Majiyar ta kara da cewa da tuni an yi bikin amma saboda rashin kasancewar mahaifiyar Yusuf, hajiya Aisha Buhari, wacce ta dawo daga Dubai inda ta kwashe watanni shida.

“Tun da yanzu ta dawo ana gab da azumi, lallai za’a yi daurin auren bayan Sallah,” majiyar ta kara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: