Labarai

Dan Sarkin Dass Mai Shekaru Shida Ya Wakilci Mahaifinsa A Wurin Taro

Daga Al-ameen Gidado jada

Sarkin Dass dake jihar Bauchi Othman Bilyaminu Usman, ya samu wakilcin dansa dan shekarar 6 a wurin taron kaddamar da shugabannin kungiyar majalisar matasa ta kasa reshen jihar Bauchi da aka gudanar a otal din Zaranda dake Bauchi.

 

An gayyaci sarkin domin ya shaida bikin, kana ya karbi takardarsa ta mukamin uban kungiyar.

Dansa dan shekara shida wanda yayi shiga irin ta sarauta tare da rakiyar fadawa da dogarawa shine ya wakilci sarkin, hakan ya jawo hankalin mahalarta taron sosai.

Mai gabatar da taron wanda ya gabatar da yaron dake zaune a kujerar da aka tanadarwa sarkin inda yace yaron yana wakiltar sarkin ne wanda zai halacci taron daga bisani.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa mutane sun ta dokin zuwa daukan hoton yaron lokacin da suka ji ance shine yake wakiltar sarkin mai daraja ta daya.

Kafin karshen taron sarkin ya halacci wurin taron inda ya karbi takardarsa tasa, amma duk da haka yaron ya cigaba da jan hankalin mahalarta taron.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: