Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Katsina Ta Tsakiya Ya Gyara Asibitin Da Ta Shekara 40 Da Ginawa A Rafin Dadi

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Zan Cigaba Da Ba Da Guddumuwar Cigaban Jihar Katsina Da Gidauniyata Ta Mai Raba Alheri

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Talla

Dan majalisar Tarayya mai wakilitar karamar Hukumar Katsina ta Tsakiya, Honorabul Sani Aliyu Danlami kuma Garkuwan Arewa ya bayyana dalilan da suka sa ya yi tunanin gyara asibitin Malam Barau da ke cikin garin Katsina bayan ta shafe shekaru fiye da arba’in da ginawa kuma baa taba yi Mata wani gyara ba tsawon lokacin.

Asibitin tana da bangarori guda hudu, wanda fiye da unguwanni bakwai ne suke amfana da wannan asibiti wanda babu wani dan siyasa komai kudi ko Gwamnatin da ta taba tunanin sake mata fasali ko daukaka darajarta na tsawon wadannan Shekaru.

Kamar yadda RARIYA ta gano cewa Gidauniyar Mai Raba Alheri karkashin jagoranci Dan Majalisa Honorabul Sani Danlami (Garkuwan Arewa) ta yi rawar gani wajan amsa koke unguwanni da wannan asibiti ta shafa wajan sake ginata da kuma daukaka darajarta domin ta yi kafada-da-kafada da sauran asibitocin zamani.

Wannan aiki dai ya xauki lokaci ana gudanar da shi inda har wasu ke tunani ko dai ba zaa cigaba da shi ba, irin yadda ‘yan siyasa ya fara aiki amma ya bari, da yake abin ya fada hannu wanda ke yi ne, sai bayan da ya fadi zaben fidda gwani na dan majalisa sannan aka kammala shi.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Shima da muke tattaunawa da shi Honorabul Sani Danlami (Garkuwan Arewa) ya shaidawa RARIYA cewa dalilin da yasa ya ba aikin gyara wannan Asibiti ta Malam Barau dake Rafin Dadi shi ne saboda mahimmacin yin hakan sannan kuma ganin yadda Gwamna Aminu Bello Masari ya dauki bangaran kiwon lafiya da mahimmci a gwamnatinsa.

Garkuwan Arewa ya cigaba da cewa “gyaran asibitin ya lashe zunzurutun kudi fiye da naira miliyan ashirin, domin dai kwalliya ta biya kudin sabulu domin maidata dai dai da zamani.

A Lokacin da RARIYA ta kai ziyarar a wannan asibiti da take Rafin Dadi ta lura da shi ne, alummar na matukar farin cikin wannan aikin kuma sun kagara a kamalla wannan aikin domin fara amfani da shi.

Haka Kuma wasu kuma da muka zanta da su kamar su yi kuka idan suka tuna da cewa ba Honorabul Sani Aliyu Danlami ne ba zai cigaba da Wakiltar su a zauren majalisar tarayyar ba , sai dai suna yi mashi fatan alheri, da wannan gidauniya ta Mai Raba alheri.

‘’Mu dai a wannan unguwa ta Rafin Dadi babu abinda za mu cewa Hon. Sani Danlami Sai Allah Ya yi masa sakayya da gidan aljanna, da Kuma bashi wata kujera domin cigaba da Tallafawa al’umma. Muna so ku gayawa duniya cewa mu ‘ya Rafin da jama’ar Katsina ta taskiya ba mu yi da na sanin tura Sani Danlami Majalisar tarayya ba kuma har abada ba zamu yi ba’’ inji wani Dattijo

Duk da cewa ya sha kalubale akan gyara da daukaka darajar wannan asibiti, hakan bai karya masa gwiwa ba, wajan ganin an kammala aikin. Yanzu abinda kawai ya rage shi ne, a sa lokacin da mai girma gwamna Aminu Bello Masari zai kaddamar da wannan Katafariyar asibiti ta zamani.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: