DAN KWALLON NIJERIYA, ABDULLAHI SHEHU YA BAIWA KUNGIYAR IZALA KYAUTAR SABUWAR MOTA DOMIN CI GABA DA YADA ADDINI
Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto
Shahararren Dan kwallon Nijeriya dan asalin jahar sokoto Mai taka leda a kasar Turkiya a kungiyar Bursaspor ya baiwa kungiyar Izala tallafin mota sabuwa domin cigaba da yada addinin Allah a ciki da wajen jihar Sokoto.
Wannan taimakon ya zo ta karkashin shugaban kungiyarsa ta bada tallafi wato, Ahmad Tijjani, wanda ya jagoranci sauran masu ruwa da tsaki na kungiyar, domin kai motar ga shugaban kungiyar izala na reshen jahar Sokoto dake Unguwar Rogo cikin birnin jahar Sokoto.
Da yake karbar mukullin motar, shugaban kungiyar izala reshen jahar sokoto Sheikh Malam Auwal Romo, ya yaba sosai bisa wannan alkawari da Abdullahi Shehu ya cika na baiwa kungiyar mota, kuma ya yi masa addu’a tare da rokon Allah ka kara yi masa gata da jagora ga dukkanin lamarinsa.
Sannan ya kara cewa “a matsayinmu na Malamai za mu kara zage damtse wurin wayar da kan jama’a dangane da muhimmancin zaman lafiya, da hadin kai a tsakanin ‘yan jiha da ma kasa baki daya domin kyautata zaman takewa.
Daga karshe ya roki Allah ya sa wannan motar da ya bayar dan yin hidima ga addinin Allah, ta zama sanadiyar kara daukakarsa da kuma tsira a ranar gobe kiyama.
Daga Aliyu Hungumawa Sak