Kimiyya

Damisan da ya yi tafiyar kilomita 3,000 don yin barbara a Indiya

Damisan ya kammala tafiya mafi tsawo da wani dabba irin sa ya taɓa yi a Indiya sannan ya samu mafaka a wani gandun daji, inda shi kaɗai ne kawai babban damisa a wajen.

Jami’an gandun daji suna kiran damisan mai shekara uku da rabi da suna Walker, kuma ya bar gandun namun dajin da yake rayuwa a can ne da ke jihar Maharashta da ke yammacin ƙasar a watan Yunin bara. Ga alama ya tafi neman yin barbara da kuma abinci ne.

Damisan wanda aka sa masa wata sarƙa a wuya, ya yi tafiyar kilomita 3,000 inda ya ratsa yankuna bakwai a jihar Maharashtra da jihar Telangan da ke maƙwabtaka da ita cikin wata tara, kafin daga bisani ya samu wajen zama a wani gandun dajin da ke Maharashtra a watan Maris. An cire masa sarƙar wuyan a watan Afrilu.

Gandun dajin Dnyanganga mai faɗin murabba’in kilomita 205, daji ne mai ɗauke da damisa nau’in rabbi da aladen daji da ɗawisu, sai dai Walker ne kaɗai damisar da ke rayuwa a dajin, in ji jami’an gandun daji.

“Bai da wata matsala ta iyaka, kuma yana samun abinci kan kari,” in ji Nitin Kakodkar, wanda wani babban jami’in gandun daji ne a Maharashtra, a wata hira da BBC.

A halin yanzu, jami’an gandun daji sun fara tunani kan ko su kai macen damisa zuwa dajin domin bai wa Walker abokiyar zama.

Sun bayyana cewa damisa ba irin dabbobin nan ba ne da za su iya su yi ta rayuwa su kaɗai ba, ba tare da barbara ba. Sai dai a cewarsu, kai wata damisa zuwa dajin ba zai zama abu mai sauƙi ba.

“Ga wasu, wannan ba babban gandun dabbobi ba ne. A zagaye yake da gonaki. Haka kuma idan Walker ya samu ‘ya’ya a wannan dajin, dabbobin da ke dajin za su kasance cikin barazana, haka kuma ‘ya’yan damisan za su yi ƙoƙari su warwatsu.”, in ji Mista Kakodkar.

Indiya ce ke da kashi 25 cikin 100 na muhallin damisa, haka kuma ƙasar ke da kashi 70 cikin 100 na duka sauran Damisoshin daji, tare da kusan dabbobi dubu uku. Adadin yawan damisa, sai dai muhallinsu ya ragu, haka kuma abincinsu ma hakan, in ji masana.

Kowane damisa guda na buƙatar aƙalla dabbobi 500 a muhallinsa domin tabbatar da wadataccen abinci, in ji masana.

An saka wa Walker wata na’ura a wuyansa tun a Fabrairun bara, inda a hakan ya ci gaba da yawo a cikin daji har lokacin daminsa, inda har ya samu wuri mai kyau ya yada zango.

Jami’an sun bayyana cewa damisan ba wai ya tafi ɗoɗar zuwa wurin da ya je ba ne, sun ce a zagaye-zagayensa, sai da ya je wurare kusan 5,000.

A lokacin hunturu da wannan bazarar, an ga Walker na kai da kawowa cikin gonaki tare da ratsa koguna da rafuka da manyan hanyoyi.

Lokacin hunturu lokaci ne da ake noman auduga a Maharashtra, wanda tsawon shukar auduga kan sa damisa ya ɓoye a yayin da yake tafiya a cikin gonaki.

Sun bayyana cewa damisan ya fi tafiya cikin dare, inda yake kashe aladun daji da kuma shanu domin ya samu abinci.

Sun bayyana cewa ya taɓa arangama da mutane sau ɗaya, inda bisa kuskure damisan ya ji wa wani mutum guda ciwo, wanda mutumin daga baya ya bi diddigin damisan har zuwa inda yake zama.

Mutumin dai ya samu tsira sakamakon raunin da ya samu duk da cewa ba wani rauni bane mai tsanani ba.

“Wannan na nuna cewa duk da ƙaruwar bil adama da ake samu a yanbkin Maharashtra, har yanzu damisa za su iya rayuwarsu a ƙauyukan yankin ba tare da takura sosai ba.

”Ci gaba a yankin bai zama ƙalubale ba da zai hana wata daba daga yin motsi ba,” Inji Dakta Bilal Habib, wanda wani ƙwararre ne ta fannin ilimin hallitu da ke aiki da cibiyar namun daji ta Indiya a hirarsa da BBC.”

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement