Daman Turai Ce Ta Tirsasa Mu Yada Wahabiyanci A duniya

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Yarima mai jiran gado na masarautar Saudiyya, Muhammad bin Salman ya bayyana cewa, kasashen Yamma abokan ittifakin Saudiyya ne suka tirsasa su yada Wahabiyanci a duniya da zummar ganin bayan Tarayyar Soviet a lokacin yakin Cold War.

Bin Salman ya furta wannan kalamin a yayin wata ganawa da yayi da manema labaran jaridar The Washington Post ta Amurka, a yayin da ya kai ziyara wannan kasar,

Talla

Yace “Kawayen Saudiyya na yammacin duniya ne suka Tirsasa masarautarmu yada wahabiyanci, gina makarantun Islamiyya da masallatai, a tsakiyar karni na 20 don hana tarayyar Soviet samun gindin zama a kasashen Musulmai.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Makudan bilyoyin dalolin da muka zuba don yada wannan akidar sun fito ne daga kungiyoyi, hukumomi da ma’aikatu masu zaman kansu da ke kasarmu. Sarakunan Saudiyya da suka gabata sun aikata babban kuskure.Yanzu lokaci ne da ya kamata a ce mun gyara kura-kuranmu”.inji shi

Jaridar Al watan ta tabbatar da sahihancin wannan bayanin na Yarima.

Madogara : Shafin Trt Hausa

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: