Raayi

Dalilina Na Son A Sake Zaben Gwamna Ganduje, Inji Sheik Kabiru Gombe

Sheik Kabiru Gombe ya yi kira ga al’ummar jihar Kano akan su sake zaben Dr Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gwamnan jihar Kano karo na biyu.

Malam Kabiru Gombe ya ce Allah ma ya sani yana da dalilin da ya sa ya ce a sake zaban Ganduje a matsayin gwamnan jahar Kano kuma yana kyautata zaton Allah ma zai yadda da dalilin shi.

Malam Kabiru Gombe ya fadi kadan daga cikin dalilin da ya sa yace al’umma su sake zaben Ganduje.

Sheik Kabiru Gombe ya ce kaf Nijeriya babu wani Gwamna da yake kan kujerar Gwamnan ya tsaya musuluntar da Maguzawa sai Ganduje.

Malam Kabiru Gombe ya kara da cewa Ganduje ya musuluntar da Maguzawa sama da dubu 20.

Malam Kabiru Gombe ya ce kwanakin baya Ganduje ya gayyace su jihar Kano domin su Musuluntar da Magujawa dari biyu.

Wallahi Saida yayi kuka domin ya ga abinda bai taba gani ba.

Malam ya kara da cewa “abinda zai kara birge ka shine duk wanda Ganduje ya musuluntar sai ya bashi sana’a domin ya tsayu da kafafunsa.

Shehin Malamin ya fadi hakan ne a wani bidiyo a lokacin da ya amsa gayyatar da Gwamna Ganduje ya yi masa na musuluntar da Maguzawa a Kano.

#Rariya

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement