-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Dalilin Da Yasa Nake Neman Karin Shekaru 4 Akan Mulki –Buhari


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace yana neman tazarce a zaben 2019 ne domin ya karfafa nasarorin da ya samu wajen yaki da cin hanci da rashawa, rashin tsaro da kuma tabbatar da ci gaban tattalin arziki.

Buhari ya bayyana hakan ne a wani taro da gidauniyar MacArthur tare da kafofin watsa labarai na NTA da DARIA suka shirya a Abuja a ranar Laraba, 16 ga watan Janairu.

Yace jam’iyyar APC ta zabe shi a matsayin dan takarar shugaban kasa saboda ya cika alkawaran zaben da ya dauka na jam’iyyar.

Kan zargin cewa akwai bangaranci a yaki da rashawa, Buhari yace zargin ba gaskiya bane.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 653

- Advertisement -

A cewarsa, babu wani da aka zarga da rashawa tare da hujja sannan suka dauke idanunsu.

Shugaban kasar yace yana taka-tsan-tsan saboda ba za a iya kama mutane cikin sauki ba a gwamnatin damokradiyya sannan akai su kotu ba tare da kwakwarar shaida ba.

Buhari ya yi kira ga yan Najeriya da su tallafa wa gwamnati sannan su tona mutane, kungiyoyi da kamfanoni masu aikata rashawa.

A cewarsa za a mika wadannan mutane ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) sannan ya Kara da cewa sun aminta da tsarin da za a bi akan lamarin.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: