Uncategorized

Dalilin Da Yasa Nake Kalubalantar Gwamnatin Buhari

Daga Khadija Garba Sanusi

Siyasa Rigar Yanchi Kowa Yana Da Ra’ayinsa Na Kashin Kansa Kuma Dokar Kasa Ta Bashi Damar Bayyana Wannan Ra’ayin Nasa Matukar Baici Mutuncin Kowa Ba, Wannan Na Kunshine Cikin Kundin Tsarin Mulkin Nigeria a Sashi Na 29 Don Haka Dole Mu Fadi Gaskiya Akan Shugabannin da Mune Muka Zabesu Da Hannayenmu Bisa Alkawarin Zasu Tura Cigaban Rayuwarmu Zuwa Mataki Na Gaba Amma Sai Mukaga Sabanin Haka.
~
A wannan Yanki Na Arewa Anjima Anayin Shugabannin amma Sai Suyi Shakulatun Bangaro Da Bukatunmu Suje Can Kudu Su Dinga Bararraka Musu Aiki, Saboda Kawai Suna Tsoron Kada Su Tada Musu Husumiyya Saboda Su Basu da Hakuri Mukuma Da Yake An Raina Mana Hankali Kullum Ayi Ta Cewa Muyi Hakuri-Hakuri ai Mu Musulmai Ne Muna da Hakuri Da Juriya Dakuma Yadda Da Kaddara, Shikenan a Haka Gwamnati Zataci Ta Cinye Yan Arewa Basu Samu Komai Ba.
~
Gwamnatin Buhari Ita Kadai Ce Gwamnati Wacce Duk Wani Dan Arewa Yayi Ammanar Itace Sanadiyyar Kubutar Da Wannan Yanki Na Arewa Daga Duk Wani Hali Da Yake Ciki, Tun A shekara Ta 2003 Buhari Yake Fitowa Takarar Shugaban Kasa Kuma Tun Wannan Lokaci Dan Arewa Ya Sallama Cewa Buhari Ne Maganin Matsalolinsa A Gwamnatance Don Haka Talakan Nigeria Ya Riga Ya Sallama Rayuwarsa Ga Gen. Muhammad Buhari har sai Inda Karfinsa Ya Kare Indai Akan wannan Bawan Allan Ne.
~
Yanzu Ahamadulillahi Gen. Buhari Shine Shugaban Kasa Kuma Bisa Jajircewar Yan Arewa Da Kuri’unsu Da Addu’insu Da Sadaukar Da Rayukansu Amma Abun Takaici Shi Kansa Wannan Mulkin Yana Neman Yaci Ya Cinye Yan Arewa Basu Samu Komai Ba, Wata Jihar Wallahi Block Na Naira 120 Guda Daya Buhari Bai Ajiye Ba Gashi Mulki Ya doshi Shekara 3, Kuma Kamar Yadda Na Fada Buhari Shine The Last Hope Na Yan Arewa Wanda shine Suke Ganin Zanyi Musu Maganin Matsalolinsu Amma Abun Yazama Tamkar Cin Kwan Makauniya.
~
Idan Kayi Tambayar Cewar Ina Aikin Buhari A Arewa Sai Ace Maka Wai Yan Inganta Tsaro Eh Haka ne Tabbas A zamanin Mulkin Buhari Mun Samu Tsaro Daidai Gwargwado Kuma Muna Godiya Ga Allah da Kuma Gwamnatin Buhari Da Ta Inganta Tsaro, Amma Ku Sani Dama Su Makiyan Yankin Arewa Abunda Sukeso Kenan Tun Kafin Buhari Ya Hau Mulki Su Kawo Wata Sarkakiyya Wacce Zata Dagulawa Talakawan Arewa Lissafi Ya Daina Tunanin Komai Sai Neman Warwarewar Wannan Sarkakiyya Kuma Shine Abunda Ya Tabbata Yanzu Talakan Arewa Hankalinsa Ya Gushe Gaba Daya Daga Kan Duk Wani Cigaban Yankin Arewa Shi Tsaro Kawai Yake Bukata a Bashi Kuma Buhari Yabashi Tsaro Don Haka Ba sai Yayi Komai Ba na Cigaban Arewa Wanda Na Tabbata A Ayu Buhari Yabar Mulkin Dawo Da Boko Haram Ba Wahala Bane Ga Makiyan Arewa Tunda Shi Buharin Ba Tabbata Zaiyi akan Mulkin Ba.
~
Yaki Da Boko Haram a Arewacin Nigeria Bai Hana Gwamnatin Buhari Yin Manya-Manyan Ayyuka a Kudanci Nigeria Ba Kaje Kaga Yadda Ake Tafka Ayyuka a Kudancin Kasar Nan A Gwamnatin Buhari Ko A Watannin Da Suka Shude Ministan Ayyuka Yaje Ganin Wani Katafaren Titi da Ake Lailayawa a Wata Jiha a Kudancin Kasar Nan, Fada da Boko Haram Bai Hana Gwamnatin Buhari Daukar Ma’aikata Ba Daga Kudancin Nigeria, Kwanakin Baya Gwamnatin Buhari Ta Debi Wasu Matasa Guda 30 Wanda Ta Hanunsu ne Duk Wani Ci Gaban Matasan Nigeria Zai Bullo A Gwamnatance Amma Abun Takaici Acikin Wadannan Matasa Mutum 2 ne Kacal Musulmi Yan Arewa Kai Ko Maganar N.Power Da Ake Ta Zuzutawa Mutane Nawa Ne Daga Arewa Suka Samu Sannan Mutane Nawa ne daga Kudancin Nigeria Suka Samu? Karamin Misali Shine A Arewa Jihar Bauchi Itace Tafi Ko Wacce Jiha Ta Samu Dubu Arba’in(40,000) Amma Idan Kaje Kudu Jihar Rivers Tana da Mutane Dubu Dari(100,000) Kunga Kenan Har Yanzu Tana Jika Kunamar Bebe Yan Kudun dai Sune Gaba da Mu Kuma Aikin Ma Shekara Biyu ne Kacal Idan Kasamu Aiki Shikenan Idan Baka Samu Ba Kuma a Koma Gidan Jiya.
~
Maganar Gaskiya Anan Itace Hanyoyin Da Shugabbanin Baya Sukabi Wajen Inganta Rayuwar Yan Kudancin Nigeria Itace Yakamata Shugabannin Yanzu Subi Wajen Inganta Rayuwar Yan Arewacin Nigeria, Duk Irin Rikicin Da Za’ayi Ya Zama Dole Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammad Buhari Ta Kakkafa Mutanenmu na Arewa a Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya A Watsasu Su Shiga Ko Ina Lungu Da Sako, Wajibine Ga Gwamnatin Buhari Da Ta Maido Da Yashe Kogin Niger Wanda Gwamnatin Yar’ Adu’a Ta Fara Ya Zamto Jiragen Ruwa Suna Zuwa Arewa Sauke Kaya, Wajibine Ga Wannan Gwamnati Ta Inganta Harka Noma Sosai da Sosai Bawai a Baki kawai ba Aje A Bawa Manoma Taki Hanu da hanu Ba Wai a Bawa Wani Mai Babba Da Jaka Ba Ya Handame, Abawa Manoma Basussuka a Wadatasu Da Kayan Noma Na Zamani, Kogunan Da Muke Dasu a Arewa a Son duk Dabarar da za’ayi Aga Cewa Ana Amfani Dasu Wajen Noma Da Rani, Ko Wacce Jiha Yakamata Ace Akwai Wani Kamfani Na Sarrafa Kayan Noman Da Ake Nomawa a Wannan Jihar, Yazama Dole a Wannan Gwamnati Titunan Arewa Da Suka Zame Tarkon Mutuwa A Gyarasu, Wajibi Ne a Gina Makarantu Isassu a Wannan Yanki Na Arewa Tun Daga Kan Primaries Har Zuwa Universities kamar Yadda Yake a Yankin Kudu domin Maganin Cunkoso a Azuzuwa don koyon karatun Hankali Kwance, Wajibi Ne Gwamnatin Buhari Ta Yi Tsari Mai Kyau Wajen Tsaida Kayyadadden Farashin Kayayyaki a Kasar Nan Domin Inganta Harkar Kasuwanci Wanda Shine Tutiyar Mutanen Arewa,Wajibi Gwamnatin Buhari Ta Nuna Cewar Dan Arewa Yana Da Kima a Wurinta Ta Hanyar Kare Masa Duk Wani Mutunci Nasa Da Dan Kudu Ya Nemi Ya Zubar Masa Misali Irin Tozarci Da Wulakanci Da Yan Arewa Suke Fuskanta a Kudancin Nigeria Dole Ne a Kawo Karshensa Tunda mu Anan Yankin Arewa Bamayi Musu Haka, akwai Dirkoki Da Yawa Na Cigaban Arewa Wanda Wajibi Ne Buhari Ya Kafasu Sosai Yadda Zai Zamanto Ko Bayan Shudewar Gwamnatinsa Babu Wanda Ya Isa Ya Ture Wannan Dirkokin Kuma Ko Ba Dade Ko Bajima Wani Dan Arewa Irin Buharin Zaizo Ya Dora Gini Akansu Shi Kansa Buhari yafini Sanin Akan Dirkokin Da Nake Magana.
~
Daga Karshe Ina Kara Jan Hankalin Yan Arewa Da a Daina Amfani Da Addininmu Ana Raina Mana Hankali Wai Cewa Mu Musulmi Ne Mun Yadda Da Kaddara Don Haka Komai Akayi Mana Babu Komai Kada Mu Daka Ta Yan Kudu Su Basu Da Hakuri Kuma Basu Da Tawakkali To Kwata-Kwata Abun Ba Haka Yake Ba, Gwamnatin Nigeria ba Akan Tsarin Musulunci Aka Kafata Ba Don Haka Mun Zabeta Kuma Dole Tayi Mana Aiki Kamar Yadda Takewa Makotanmu Aiki, Wallahi Andaina Yaudararmu Da Musulunci Domin Shi Kansa Musulunci Yayi Hani Da Bangaranci, Idan Kuma Yan Kudu Tsoronsu Akeyi Shiyasa Akeyi Musu Ayyuka To Muma Lallai Yakamata Mu Fara Bawa Gwamnati Tsoro Domin Ta Gudanar Mana Da Ayyuka, Tunda MakaoYace Baison Ana Ganinsa Ba Sai Andungureshi.