Dalilin Da Yasa Muka Yiwa Buhari ihu -`Yan Majalisar PDP

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Daya daga cikin mambobin majalisar wakilai ‘yan jam’iyyar PDP ya bayyana cewar sun yiwa shugaba Buhari ihu ne domin nuna rashin jin dadinsu bisa yadda gwamnatin tarayya ta gaza yin aiki da kasafin kudin shekarar 2018 kamar yadda ta gabatar.

A jiya, Laraba, ne wasu mambobin majalisar wakilai suka yiwa shugaba Buhari ihu yayin da ya isa zauren majalisar domin gabatar da kasafin kudin shekarar 2019.

Talla

Da shigar Shugaba Buhari zauren majalisar sai wasu mambobi suka kaure da ihun “noooo”,”noooo” tare da yin ihun “karyane”, “karyane” lokacin da Buhari ya fara zayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu.

Da yake ganawa da manema labarai bayan kammala gabatar da kasafin, shugaban wata kungiyar ‘yan majalisar tarayya Jam’iyyar PDP, Chukwuma Onyema, ya bayyana rashin jin dadin ‘yan majalisar a kan yadda bangaren zartarwa ke nuna son a kai wajen zabar aiyukan da zata kaddamar daga cikin wadanda ta gabatar a kasafinta na shekarar 2018.

Kazalika, ya bayyana cewar hatta yajin aikin da ma’aikatan majalisar ke yi na da alaka da rashin kaddamar da kasafin kudin shekarar 2018.

Talla
Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Tunda safiyar jiya laraba ne dai mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ministoci da hadiman shugaba Buhari masu yawa suka isa zauren majalisa domin gabatar da kasafin kudin shekarar 2019.

Osinbajo da hadiman sun isa zauren majalisarne da misalin karfe 11:50 na safe, yayin da ake sa ran shugaba Buhari zai iso zauren majalisar da misalin karfe 12:00 na rana.

Sai dai wasu rahotannin da suka iso mana sun bayyana cewar sanatoci sun fara zaman majalisa bayan gajiya da jiran karasowar shugaba Buhari.

#Jaridar Damokoradiyya

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: