Dalilin Da Yasa Ba Zan Kara Yin Korafi Da Gwamnatin Da Na Kada Ba -Buhari

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar ba zai kara yin korafi da gwamnatocin baya na jam’iyyar PDP da suka haddasa matsalolin da yanzu gwamnatinsa ke fuskanta ba.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake bayyana takaicinsa dangane da matsalar cin hanci da rashawa ga’yan Najeriya mazauna kasar Poland.

Talla

Mai taimakawa shugaba Buhari a harkokin kasashen ketare, Abike Dabiri-Erewa, ce ta shirya taron domin bawa ‘yan Najeriya mazauna kasar Poland damar ganawa da jami’an gwamnatin Najeriya domin tattaunawa a kan al’amuran da suka shafi mulki.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Yace “Mun gaji matsaloli masu yawan gaske; sai dai na riga na yi alkawarin cewar zan daina korafi a kan hakan saboda ni na daukowa kaina aikin shugabancin Najeriya.

“Sau uku ina takarar takarar neman zama shugaban kasar Najeriya kafin na samu a karo na hudu, saboda haka yin korafi ba nawa bane.”Babu wanda ya tilasta min sai na zama shugaban kasa. Sau uku ina zuwa kotu a kan zabe. Amma a karo na hudu, da taimakon Allah da na fasahar na’urar tantancewa, sun kasa yin magudin da suka yi min, nayi nasara a kansu,” a kalaman Buhari. 

#Mikiya

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: