Kannywood

Dalilan dayasa Naki Fitowa A Yar Madigo Film Din Nollywood – Rahama Sadau

Dandalin Kannywood: An so in fito a yar madigo a wani fim din kudu amma naki amincewa – Rahma Sadau

Korarriyar shahararriyar jarumar fina-finan nan na Kannywood a da yanzu kuma hadda fina-finan kudu Rahma Sadau ta bayyana cewa an so ta fito a wani fim din ta na fina-finan kudu a matsayin yar madigo amma sai ta ki yadda saboda la’akari da daga inda ta fito watau arewa.

 

Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wata fira da tayi da jaridar The Guardian a karshen makon jiya inda kuma ta bayyana cewa tayi haka ne kawai bisa la’akari da daga inda ta taso da kuma martaba al’ada da addinin yankin arewa.

NAIJ.com kuma dai ta samu cewa da take tsokaci game da korar ta da kungiyar fina-finai tayi, Rahma Sadau tace ita wannan korar ma gaba ta kaita don kuwa yanzu idon ta ya kara budewa kuma ta kara samun wasu damammaki na gudanar da sana’arta a dukkan fadin duniya.

Haka nan kuma jarumar ta bayyana rungumar da tayiwa mawaki ClassiQ da tayi sanadiyyar korar tata a matsayin bangaren aikin ta da bai kamata a tsangwameta ba game da hakan.

Daga karshe ne kuma sai jarumar ta kara jawo hankalin mutane da cewa shifa tsoron Allah a zuciya yake don haka ba dai dai bane ba a rika yi mata kallon ‘yar iska don kawai tana sana’ar ta.

Shin Meye Ra,ayinku Akan Haka

Hausa.naij.com

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.