Dalilan Da Ya Sanya Muka Rufe Ofisoshin Jaridar Daily Trust Na Abuja Da Maiduguri, Da Kama Ma`aikatan Su -Rundunar Sojin Najeriya
Mun dauki matakin rufe Ofisoshin Jaridar ne dake Abuja da Maiduguri, da kuma wasu daga cikin Ma’aikatan Jaridar, biyo bayan wani labari da jaridar ta wallafa a ranar Lahadi, inda take fallasa wani shiri na Rundunar Sojin Najeriya, akan murkushe Kungiyar Boko Haram, wanda hakan ya ci karo da bayanan harkar tsaro ta kasa, kuma a hannu guda ankararwace ga Kungiyar Ta’adda ta Boko Haram kariya ga kansu akan matakan da rundunar Soji zata dauka a kansu.
Bayanin haka na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da rundunar Soji ta fitar wacce ta samu sanya hannun Mai magana da yawun Rundunar Birgediya Sani Usman Kuka Sheka, aka rarrabata ga manema labarai a jiya Lahadi.
- Advertisement -
Rundunar Sojin ta bukaci ‘yan Jarida da sauran Jama’a da bada goyon bayan da ya dace wajen taimakon Rundunar Soji domin karasa kawar da Boko Haram a kasar nan, sannan ya kara da cewar gayyatar ‘yan Jaridar da rundunar tayi ba wai an yi hakane domin tauye hakkin ‘yanci magana ko aikin Jarida ba, sai dai an yi hakane domin tabbatar da tsaro da kuma kaucewa fallasa asirin tsaro na kasa ta hanyar da bata dace ba.
Rundunar Sojin ta tabbatar da cigaba da gudanar da kyakkyawar alaka a tsakanin da ‘yan jaridu a fadin tarayyar kasar nan, kasancewar su abokanan tafiya a wannan gagarumin aiki da akeyi na kawar da Boko Haram a fadin kasar nan.