-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Dalilan Da Suka Sanya Na Shekara 13 Ban Shiga Amurka Ba -Atiku


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

A fiye da shekaru 13, Alhaji Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma yanzu dan takarar shugabancin kasar karkashin jam’iyyar PDP ya guji Amurka.

Akwai lokacin da Amurka din ta hana shi Visa. Amma a ranar alhamis sai gashi ya sauka a birnin Washington DC don tattaunawa da wasu jami’an Amurka akan yakin neman zaben shi a Najeriya.

Ziyarar wacce tsohon mai gidan shi Olusegun Obasanjo da wasu magoya bayan shi suka assasa, ya jawo tambayoyin dalilin da yasa Atiku ya guji zuwa Amurka tuntuni.

Abinda ya faru a shekaru 9 da suka wuce, akwai wani kwamitin majalisar Amurka da ya bada rahoto akan almundahanar kudi akan shi wanda ya hada da karbar cin hanci daga Siemens.

Kwamitin da sanata Carl Levin ya jagoranta ya bayyana illolin rashawa a cigaban gwamnati, dokokin damokaradiyya da dokokin shugabanci.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 653

- Advertisement -

Kwamitin ya mika rahoton ne a 4 ga watan Fabrairu 2010, shekaru uku bayan da Abubakar ya sauka daga kujerar shi ta mataimakin shugaban kasa.

Rahoton ya bayyana taka dokokin Amurka da Abubakar tare da matarshi ta hudu, Jennifer Doughlas suka yi.

Ya kuma bayyana cin hancin Siemens da ya shiga daya daga cikin asusun bankin shi. Wannan shine tushen abinda yasa aka hana Abubakar shiga kasar Amurka.

#Mikiya

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: