Dalilai 11 Da Su Ka Sa A Ka Gaza Murkushe Boko Haram

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Akalla yakin Boko Haram ya kai shekara 10 kuma an kashe soja da ’yan sanda da dama, an kashe jama’ar gari wadanda ba za mu iya sanin adadinsu ba a Najeriya; wannan sai Allah. Sannan sakamakon wannan yakin ‘yan gudun hijira sun fi miliyan biyu. Wannan yakin ya lalata al’amuran rayuwa ta kowacce fuska.

Shin Ba Za A Iya Kawo Karshensa Ba? Amsa ita ce; za a iya, amma ta hanyar gano dalilan da su ka hana a murkushe shi, kamar haka:-

Talla

1-Dalili na farko; rikicin Boko Haram ba na siyasa ba ne da tattalin arziki da soja, rikicin addini ne na malamai da kwakwalwa, wadanda su ne ahalin da za su yi yakin sun kauce, an bar wadanda ba ahalinsa ba su na shan wahala sun kasa gano bakin zaren.

2- Na biyu; akasarin yara matasan soja da ‘yan sanda da su ke fada da Boko Haram, ba su shiga aikin ba don su mutu su taimaki Najeriya, su kare ta daga duk wani mugu ba; sun shiga aikin ne domin babu aikin yi a kasar. Aikin soja da dan sanda a gurinsu hanyar cin abinci ce kawai. Babu shirin mutuwa daga gare su.

3- Na uku; idan dan Boko Haram ya mutu a filin daga, a ganinsa aikin Allah ya ke yi kuma aljanna zai tafi, su kuma sojojinmu da ‘yan sandanmu an zare mu su kishin kasar daga zukatansu, kuma idan an kashe su a fagen daga, mamaikon su sami karramawa, gawarsu ma a wani lokacin cikin wulakanci a ke binne ta, sannan ba su da yakinin kulawa ta musamman daga gwamnatin Najeriya ga iyalansu idan sun mutu.

Talla

4-Na hudu; a wajen wannan yakin manyan jami’ai da su ke gudanar da shi, ba su da jituwa da juna, ba sa aiki tare, kowa tasa ce ta ke fisshe shi. Ina nufin da ‘yan sanda da soja da DSS da CJTF da ‘yan siyasa masu lura da harkar kansu ba a hade ya ke ba, yaki sai da taimako da fahimtar juna.

5-Na biyar; an saka harkar siyasa da yawa a ciki. A lokacin mulkin Goodluck Jonathan cewa ya yi kirkiro Boko Haram a ka yi don shi ba Musulmi ba ne. A yanzu kuma lokacin Muhammadu Buhari da gangan gwamnati ta ke hana a fadi labarai na gaskiya da su ka fito daga yankin, don kada jama’a su ce an gaza. An toshe bakin kowa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

6-Na shida; ma’aikatan da su ke kula da iyakar Najeriya da makwabtanta da ma’aikatan kwastom da ma’aikatan da su ke kula da tsaro na cikin gida su na karbar cin hanci suna barin barna da masu laifi, sannan suna wasa da aikinsu,wanda suke son yin aiki kuma babu kayan aiki na zamani, babu kara musu karfin gwiwa.

7- Na bakwai; makamai da kayan yaki da sojanmu su ke amfani da su an daina yayinsu sun tashi daga aiki, wadanda su ke hannunsu kuma duk da tsaffi ne, su kuma babu sabis, masu rike da su kuma wato sojojin ba a basu kulawa irin yadda yake a sauran kasashen duniya. A bisa al’ada soja a fagen daga rarrarshinsa da tarairayarsa ake yi.

8-Na takwas; wasu manya na jami’an tsaro sun maida wannan yakin harkar bizines, ba sa so a kawo karshensa. Don haka duk wata dabarar yaki ba sa amfani da wacce za ta yi tasiri da nasara, sai dai bara-gurbiya, sun maida yakin harkar kwangila da hanyar samu.

9- Na tara; duk ka’idojin da ake dora mayaka akai, an daina amfani da ita. In ana jin haushinka sai aturaka Maiduguri, in kayi laifi sai abarka ko ka cancanta ka dawo gida.

10-Na goma; an ki da gangan a tabbatar da cewa wannan matsalar tamu ce, ya kamata mu hadu mu gyarata, sai kawai a rika dorawa wasu laifin, har ma da wasu a kasashen waje. Wannan mas’alar ta Najeriya ce, ta sarakai da malamai da ma’aikata da attajirai da ‘yan siyasa da ‘yan boko da kowa da kowa. Na sha daya; idan an gano wanda ya gaza akan aikinsa ko kuma wanda ya yi wata barna sai a rufa masa asiri ko kuma a makale da wani dalili a bar shi ya cigaba da lalata al’amura don biyan wata bukata. Ni dai abin da na fahimta, in har an yadda wadannan matsaloli ne, to a gyara su, Ina da yakini za a iya samun sauki.

# leadership

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: