Labarai

Dalibin makaranta a Ogun ya kashe kansa bayan ya kashe kuɗin makarantarsa a wajen caca

Dalibin makaranta a Ogun ya kashe kansa bayan ya kashe kuɗin makarantarsa a wajen caca

 

Wani dalibin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Ilaro a Jihar Ogun, Samuel Adegoke, ya kashe kansa ta hanyar shan wani abu da ake zargin maganin kwari ne.

 

An ce marigayin ya kashe kansa ne bayan da ya yi kashe kudin makarantarsa ​​da na abokinsa a wata caca ta yanar gizo.

 

rahotanni sun bayyana cewa Adegoke, wanda dalibin Difloma ne a fannin Electrical Electronic Engineering, ya kashe kansa ne a ranar Litinin a lokacin da abokan aikinsa ke shirin jarabawar kammala zango na farko.

 

Jaridar Punch ta ruwaito cewa marigayin ya yi amfani da kudin makarantarsa ​​ne wajen yin caca ta yanar gizo a ranar Juma’a kuma ya yi rashin nasara a car.

 

Ya kuma yaudari abokinsa don samun kalmar sirri, ya kuma shiga manhajar wayar abokin, sannan ya kwashe masa kudin asusu ya yi caca da su sannan aka kuma cinye shi.

 

Mataimakin rijistara na makarantar, ɓangaren hulda da jama’a, Sola Abiala, ya tabbatar wa da jaridar faruwa lamarin.

 

Daily Nigerian Hausa