Labarai

Daliban Kwalejin Nuhu Bamali Sun Samu Ƴannci, Bayan Yin Garkuwa Da Su- Makarantar

‘Yan bindiga sun sako Daliban su shida da ma’aikatan kwalejin fasaha ta Nuhu Bamali da ke Zariya a jihar Kaduna.

‘’ An saki wadanda aka yi garkuwar da su a daren jiya Alhamis a wani wuri da ba a bayyana ba a Kaduna, ’’ in ji makarantar.

Jami’in hulda da jama’a na kwalejin, Abdullahi Shehu, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a yau Juma’a.

Shehu ya ce daliban da ma’aikatan da aka sace sun sake samun ‘yanci bayan Iyayen su da danginsu sun tattauna da ‘yan bindigar. Amma, bai faɗi takamaiman ko an biya kudin fansa ba ko a’a ba’a biya ba.

Jaridar Solacebase ta bayyana cewa ya ce hukumomin makarantar za su karbi Daliban a yammacin ranar a wurin da aka ajiye su bayan an sake su.

Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa ‘yan bindigar sun kai hari makarantar kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamali a ranar 11 ga watan Yuni, 2021, inda suka yi awon gaba da wadanda suka sace daga dakunan kwanan su da ma’aikatansu kuma sun kashe Dalibi daya yayin harin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: