Jami’ar Mewer dake ƙasar Indiya ta dauki wasu daga cikin daliban da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tura karatu Indiya, aiki.
Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin tsohon Gwamnan na Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, inda ya bayyana cewa cikin daliban da ya tura mutane 13 sun sami aiki a makarantar.
Daliban da Kwankwaso ya tura dan karo karatu, su 370 ne, mun sami labarin cewa, baya ga wadanda makarantar ta basu aiki wasu ma kanfanunuwa sun nemi suyi aiki dasu.
A kwanan nan ne dai tsohon Gwamnan ya taro wasu daga cikin daliban yayin da suka dawo daga kasar ta India bayan kammala digirin su na biyu, wanda gidauniyar Kwankwasiyya ta dau nauyi.
Daga Salisu Magaji Fandalla’fih