-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Dakatar da CJN: Matasan Arewa Sun Goyi Bayan Buhari


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Wata hadakar kungiyoyin arewa a jihar Kaduna sun bayyana goyon bayansu a kan matakin da Shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na dakatar da Alkalin Alkalan Najeriya, Walter Onnoghen inda har suka bukaci ya yi murabus daga mukaminsa.

Matasan sun fita sunyi zanga-zanga a tituna inda suke nuna rashin amincewarsu da wadanda ke nema a mayar da Alkalin Alkalan a kan mukaminsa.

Masu zanga-zangan sun zaga manyan titunan jihar Kaduna dauke da alluna da takardu masu dauke da sakonni da ke yabawa Shugaba Muhammadu Buhari a kan kokarin da ya ke yi na kawar da rashawa a fannin shari’a kuma suke shawartarsa ya cigaba da dagewa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 658

- Advertisement -

A yayin da suke magana da manema labarai, shugabanin kungiyoyin sun ce wadanda ke neman a mayar da Alkalin Alkalan makiyar Najeriya ne, sun kuma gargadi mutane da ke kokarin danganta tsige Onnoghen da kabilanci ko addini.

A cewarsu, Justice Onnoghen ya saba doka ta hanyar kin bayyana wasu kadarorinsa ga Kotun Da’ar Ma’aikata saboda haka ya dace ya yi murabus ne a maimakon ya rika kaiwa da komowa a kotu.

Matasan sun ce dakatar da CJN shine mataki na farko kuma suka bukaci ayi gaggawar sallamarsa tare da gurfanar da shi a kotu domin ya gurbi abinda ya shuka.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: