Daga Datti Assalafiy
Mayakan sojojin Nijeriya karkashin rundinar
Operation WHIRL PUNCH sun samu nasaran kama wasu mutane uku wadanda suka shahara wajen safarar makamai zuwa ga barayi da masu garkuwa da mutane, wadanda aka kama ga sunayensu kamar haka: Aminu Umar ‘dan shekara 32, Shehu Samaila ‘dan shekara 25 da Bilyaminu Abdullahi ‘dan shekara 22.
An samu nasaran cafke su ne a garin Rijau dake jihar Neja lokacin da sojoji suke duba ababen hawa, an kama su da bindigogi guda arba’in da hudu (44), da harsashin bindiga guda dari uku da hamsin da daya (351), sun boye bindigogi da harsashin a cikin mota Toyota Corolla mai dauke da rijista kamar haka ZUR 28DX Kebbi.
Bincike ya nuna; wadannan mutane uku masu safaran bindigogi da harsashi sun nufi garin Bena Danko a karamar hukumar Wasagu jihar Kebbi wanda take makwabta da jihar Zamfara inda ayyukan barayi ‘yan fashi da makamai da masu garkuwa da mutane yayi kamari, wannan kamun yayi kama da irin wanda akayi a watan da ya gabata, lokacin da aka kama wani mutum mai suna Rabi’u Akilu aka sameshi da bindigogi guda 36 da harsashi 343 ya boye a cikin mota Toyota Corolla ya nufi jihar Zamfara
- Advertisement -
Rundinar sojojin Nijeriya tana kira ga matafiya a yankin jihar Zamfara da Kebbi da su cigaba da mika bayanan sirri ga rundinar sojin Nigeria da sauran hukumomin tsaro
Wannan ba karamin nasara aka samu ba, yana daga cikin hanyoyin samun nasara wajen dakile barazanar tsaro shine a toshe duk wata hanya da masu aikata miyagun laifuka sukebi su samu kayan ta’addanci, idan barawo ko ‘dan ta’adda bai samu bindigi ba to ba zai iya zuwa ya aikata mugun laifi ba
Ya Allah Ka karawa jami’an tsaron Kasarmu Nijeriya taimako da nasara akan masu aikata munanan laifuka. Amin.