Dage zabe: Jam`iyyar PDP Za Ta Gudanar Da Muhimmin Taro A Yau Talata

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

A yau Talata, ne jam’iyyar PDP za ta gudanar da taron shugabannin ta na kasa (NEC) kamar yadda sakataren jam’iyyar, Kola Ologbondiyan, ya fitar da sanarwa.

Taron na zuwa ne bayan hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) ta daga zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da ta shirya gudanar wa ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu, zuwa ranar Asabar, 23 ga watan Fabarairu.

Talla

Mista Ologbondiyan ya bayyana cewar za a yi taron ne a hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja da misalign karfe 12:00 na rana.

Wasu Abubuwan Masu Alaka

Hukumar Karota Ta Kama Mota Cike Da Tabar Wiwi

Talla
1 of 661

Daga cikin wadanda ake tsammanin za su halarci taron akwai gwamnonin jam’iyyar da kuma kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) da sauran su.

Duk da jam’iyyar ba ta bayyana abinda za ta tattauna a wurin taron ba, majiyar mu ta bayyana ma na cewar batun daga zaben shugaban kasa da ‘yan takarar majalisar tarayya ne zai fi daukan hankali mahalarta taron.

A yau, Litinin, ne jam’iyyar APC mai mulki ta gudanar da nata taron domin tattauna batun dag zaben da INEC ta yi ranar Asabar.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: