-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

‘Daga Buharin har Atikun Duk Bana Yi’ -Inji Wole Soyinka


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Wole Soyinka, kwararre kuma sanannen marubuci yace ba zai goyi bayan yan takara biyun ba na fitattun jam’iyyun siyasar da suka fito takarar shugabancin kasa.

Yace hakan ne a zauren tattaunawa na yan kasa a na 2019.

“Lokaci ne yanzu na sabuwar alkibla kuma idan wani dan takara ya bayyana zamu bashi goyon baya,” a cewar shi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP sune yan takara biyu dake kan gaba.

Soyinka yace ” yanzu lokaci ne na canza alkiblar kasar nan ta hanyar da ya dace. “Don gujewa tantama, bari in fadi matsayata saboda bana son in zama mai harshen damo;

“Ni Wole Soyinka bazan zabi kowa daga cikin sanannun ‘yan takarar biyu ba. Na gano cewa dukkanin su basu cancanci kuri’a ta ba,” inji shi.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 660

- Advertisement -

“A saboda dalilai na wadanda ba sai na bayyana ba, banda ra’ayin su.

Matsayata mai sauki ce, itace lokaci yayi da zamu canza alkibla. Kuma kiri kiri ba ni kadai bane, akwai wata kungiya dake taro a Legas don fitar da Dan takara daya da ta yarda dashi.

Akwai wata kungiyar a Abuja ma wacce daga karshe zasu sanar damu dan takarar da ya dace.

Ana abubuwan sirri don ganin an canza akalar kasar nan ta hanyar da ta dace, kuma a ganar da mutane cewa bai kamata su bautar da kansu har abada ba ga tsofaffin dokoki.”

#Mikiya

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: