Daga Comrade M.K Soron Dinki
Mutane kashi uku ne a cikin alqarya: Yara, matasa da dattijai. A cikin wadannan rukunin babu wanda yake da tasiri wajen kawo gyara ko matsala irin rukunin matasa. Matasa dai sune kwankwason al’umma, kuma mun san cewa ko a wasan kwallo idan akace tsakiya (midfield) ta karye dole za a samu matsala.
Misalin baya wuce haka tunda nasan mafi rinjayen masu karanta rubutuna matasa ne masu buga kwallo ko zuwa gidan kallonta. Cigaban kowacce kasa yana samuwa ne idan aka samu jajirtaccin matasa masu kishi wajen samar da zaman lafiya. Rashin zaman lafiya ne yake kawo baqin talauci wanda shi kuma ya haifar da afkuwar manyan laifuka a cikin al’umma.
Babu shakka duk inda babu zaman lafiya ba a tunanin cigaba a wajen tunda sai da kwanciyar hankali zaka nemi ilimi ko sana’a a matsayinka na matashi.
To ku fada min yadda za a cigaba idan babu ilimi da sana’a. Akwai bukatar mu yi karatun ta nutsu fa, saboda da yawa daga cikinmu suna shiga motar alfa a wannan rayuwar da take bukatar nazari da aiki da hankali. Misali, lokacin da rikici yayi tsanani a Kaduna a 1992, bayan kowa yaji jiki, wasu sun rasa dukiyoyinsu da lafiyarsu, wasu kuma rayukansu da na iyalansu.
Dole saida matasa suka tashi tsaye wajen samar da zaman lafiya a karkashin jagorancin Imam Muhammadu Ashafa da Postor James Wuye. Aikin da matasan suka yi ya haifar da zaman lafiya a tsakanin musulmai da kiristocin Zangon Kataf. Kaje ka karanta tarihin abun ko akan internet ne.
A zance na gaskiya fa, ni matashi ne amma ban ga mutumin da zai sakani na tayar da zaune tsaye ba saboda cigabansa a siyasa ko a rayuwa. Ni bana son cigaba? Idan wata kujera yake kai, nima so nake na hau irinta idan har ma ba wacce ta fita ba.
To haka nake tunani akan kowanne matashi. Ku zo mu gina kasa, watakila kaine gwaunan gobe.
To saidai matasalar itace, kamar matasan basu shirya ba, wasu daga cikinmu sun koma tayar da zaune tsaye, duk sanda aka gyara Najeriya, ma