Da Gaske Ne Wata Mata Ta Rikide Ta Zama Kura A Kano?

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Abba Wada Ibrahim Gwale

Bayan na samu labarin sai na garzaya ofishin ‘yan sanda na Gwale domin tabbatar da gaskiyar labarin cewa wai wani mutum ya mayar da wata mata kura a unguwar Kofar Na’isa dake karamar hukumar Gwale.

Talla

Bayan na dauki lokacin kuma muna tare da ’yan jaridu daga gidajen radiyo da yawa na jihar Kano sai aka ce mana ba za mu samu damar yin magana da kowa ba sai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Magaji Musa Majiya ya zo.

Bayan ya zo muka shiga aka fito da wannan bawan Allah Wanda kuke gani a wannan hotuna kuma ya bayyana gaskiya abinda ya faru.

Ya ce shi dan garin Mulumfashi ne dake jihar Katsina kuma yana wasa da kura ne, sai wasu mutane suka kira shi tun daga Katsina suka ce ya zo Kano sun shirin fim da za su yi, saboda haka akwai wani fitowa (scene) da za a nuna wata mata tana kuka saboda an mayar mata da ‘yar uwarta kura.

Kuma ya zo aka fara daukar fim din har aka zo wajen da wata mata za ta yi masa ihu cewa ya mayar mata da ‘yar uwarta kura.

Lokacin da aka fara ‘scene’ din sai matar ta fara kuka su kuma mutanen da suke wajen suka yi zaton gaskiya ne shine suke rufe shi da duka kuma kurar ta kwace daga hannunsa ta shiga gari sai a hankali aka yi wayo aka sake kama ta.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Daga nan sai mutanen unguwar suka dauka abin gaskiya ne kuma suka kai shi ofishin ‘yan sanda dake Gwale.

Ita ma wadda ta yi ihun ta tabbatar da cewa daga garin Zaria ta zo kuma cewa aka yi ta zo za a yi shirin fim, amma tabbas ta ce ‘yar uwarta ba ta zama kura ba.

Sai dai har yanzu ba ta da tabbacin inda ‘yar uwar tata ta shiga har yanzu. Amma dai ta ce ba ita ba ce wannan kurar da ake magana.

Kakakin rundunar ‘yan sanda Magaji Musa Majiya ya bayyana cewa za su ci gaba da bincike sannan dole su gurfanar da su a gaban kotu.

Sai dai abin tambaya a nan shine ina Daraktan fim din?
Wanne irin fim ne?
Sannan ina ragowar wadanda suke shirya fim din tare?

Wannan ita ce kurar da kuma mai ita a ofishin ‘yan sanda na Gwale.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: