Labarai

Da duminsa: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohuwar alkalin alkalai

An nemi tsohuwar alkalin alkalai ta jihar Abia, Mai Shari’a Nnenna Oti, sama da kasa an rasa, inda ake kyautata zaton cewa masu garkuwa da mutane ne suka yi garkuwa da ita.

A cewar Bishop Chidi Collins Oparaojiaku na cocin Ohaji/Egbema Anglican Diocese, an sace Mai Shari’a Oti a ranar Asabar, 4 ga watan Satumba, a lokacin da take kan hanyarta ta zuwa jihar Anambra, kamar dai yadda jaridar PM News ta ruwaito.

Bishop din kuma ya kara da cewa wadanda suka kama tsohuwar alkalin alkalan sun bukaci a biya su kudin fansa, a rahoton da jarida The Nation ta kara.

Da yake nuna jimami kan wannan lamari, babban Malamin addinin, ya ce;

Wannan abin takaici ne, abinda ya kamata muyi shine mu cigaba da addu’a Allah ya sanya tausayi a zuciyar masu garkuwa da mutanen su sake ta.

Haka suma rundunar ‘yan sanda da suke nasu bayanin dangane da wannan lamari, sun bayyana cewa tuni sun fara bincike dangane da wannan lamari.

‘Yan bindisa sun shiga gidan dan majalisa sun sace mata da dan sa a jihar Katsina
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun afka gidan dan majalisa mai wakiltar mazabar Bakori dake jihar Katsina, Dr. Ibrahim Aminu Kurami.

Rahoton da jaridar Katsina Post ta fitar sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da matar dan majalisar da kuma dan sa guda daya a wannan hari da suka kai.

Bayan haka kuma ‘yan bindigar sun harbi wani makwabcin dan majalisar mai suna Malam Ubaidu Abbdulhakim a lokacin da yayi kokarin artabu da su.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: