Labarai

DA DUMIDUNINSA: Yadda Dakarun Abba Kyari Suka Halaka Makasan Ahmad Gulak

Daga Datti Assalafiy
Bayan ‘yan ta’addan IPOB da suka kashe Ahmad Gulak a jihar Imo sun kashe shi sun gudu, an kama direban motar da yake jansa, kuma ya bada bayanai kan wadanda suka kashe shi.

Dakarun ‘yan sanda na jihar Imo tare da dakarun IRT karkashin jagorancin DCP Abba Kyari da suke aiki a Imo sunbi bayan ‘yan ta’addan na IPOB.

‘Yan sandan sun tarar da ‘yan ta’addan a wata mahada da ake kira Enyi Ogwgu junction sun tare wata motar tirela da ta dauko albasa daga Arewa, suna ta rabarwa mutanensu albasar, da suka ankara da zuwan ‘yan sanda sai ‘yan ta’addan suka bude wuta.

Anan aka fara musayen wuta, wasu daga cikin ‘yan ta’addan sun tsere da harbin bindiga a jikinsu, yayin da wasu kuma wadanda bullet ya tabasu a cikin motarsu, motar ta kama da wuta sun kone kurmus su guda shida ‘yan ta’addan IPOB din da suka kone.

‘Yan sanda sun kwato bindigogi kirar AK47 guda 3, bindiga kirar Engilsh Pistol guda 2, Magazin na AK47 guda 5, da harsashin bindigar AK47 guda 92, sai tarkacen kayan tsafi na ‘yan ta’addan da motocinsu wadanda suke kone da wuta.

Jinjina gareka ASP Mohammed Ejily Abdulrahman Bama (Bush to Bush Commander) babban mayakin Sarkin Yaki DCP Abba Kyari, wannan wasan ya bugu mai kyau.

Alhamdulillah ko a yanzu zuciya tayi sanyi game da daukar fansa akan wadanda suka hallaka Ahmad Gulak, maganar shugaba Muhammadu Buhari ta tabbata gaskiya da yace jinin Ahmad Gulak ba zai zuba a banza ba.

Allah Ka jikan Ahmad Gulak.
Allah Ka karawa ‘yan sanda da sojoji nasara akan ‘yan ta’adda.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: