Labarai

DA DUMIDUMINSA: Mahadi Ya Yi Nasara A Shari’ar Su Da Tsohon Shugaban ‘Yan Sanda

Rahotannin dake shigo mana yanzu daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babbar Kotun tarayya ta yi fatali da karar da tsohon Shugaban ‘Yan sanda Mohammed Adamu ya shigar gabanta akan sanannen ɗan kasuwar nan mazaunin garin Kaduna Dr Mahadi Shehu, sannan kotun ta bada Umarnin biyan kudi har Naira Miliyan 5 ga Mahadi saboda bata mishi lokaci da aka yi.

Kotun ta bayyana cewar a bisa ga ‘yanci na ɗan Adam Mahadi na da damar bayyana ra’ayin shi kamar yadda dokar ‘yanci kasa ta bashi a cikin sashi na 34 da 35 na kundin tsarin mulki shekarar 1999 wanda aka sake yi wa gyaran fuska, wanda bai bada dama ga rundunar ‘yan sanda ko Shugaban ‘yan sanda na tauye shi ba.

Hakazalika Kotun ta bayyana cewar Mahadi Shehu na da dama da ‘yanci na fadin albarkacin bakin sa akan abubuwan dake faruwa a kasa ba tare da tsangwama kamar yadda yake rubuce a sashi na 38 na kundin mulkin kasa.

Tun farko dai Hukumar ‘yan sanda ta hannun tsohon shugaban rundunar Mohammed Adamu sun daukaka kara zuwa babbar kotun tarayyar inda suke ƙalubalantar Mahadi da kiren karya da bata sunan gwamnatin jihar Katsina, Lauyoyin bangarorin biyu sun fafata a tsakanin su inda aka dage saurarar karar zuwa yau Laraba 30 ga Wata Yuni na shekarar 2021.

A zaman da kotun ta yi a yau karkashin jagorancin Mai Shari’a Hamza Mu’azu ta amince da takardar koke da Mahadi ya shigar gabanta, bisa ga kwararan hujjoji inda ta yi fatali da karar sannan ta bukaci a biya shi diyya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: