-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

DA DUMIDUMINSA: An Yi Juyin Mulki A Kasar Gabon


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Hassan Bahaushe Gombe

Rundunar Sojin kasar Gabon Sun Yi wa Shugaba Ali Bango juyin mulki.

Yanzu nan mu ke samun labari daga jaridun waje cewa sojoji a kasar Gabon sun kifar da gwamnatin kasar.

Rundunar sojin kasar sun mamaye gidan rediyon da ke Gabon inda su ke ta sukar halin da shugaban kasa Ali Bango yake ciki.

Wasu Dakarun Soji a Gabon sun shiga babban gidan rediyon da ake da shi a kasar inda su ka tabbatar da kifar da gwamnati mai-ci.

Manema labarai sun tabbatar da cewa an ji harbe-harben bindigogi a babban birnin Libreville dazu da sassafe.

Sojojin kasar na Gabon sun sanar da cewa za su kafa shugabanci na rikon kwarya inda za a nada wata majalisa ta musamman da za ta ja ragamar kasar.

Sojojin sun ce za su dawo da mulkin farar hula ne bayan hambarar da gwamnatin Bongo.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 660

- Advertisement -

Yanzu haka Ali Bongo yana kasar Morocco inda yake fama da rashin lafiya tun a shekarar bara.

A farkon shekarar nan ne shugaban kasar mai shekaru 59 ya aikowa mutanen kasar Gabon sako tun bayan da ya hadu da lalurar rashin lafiya a bara.

Laftanal Kelly Ondo Obiang, wanda shi ne shugaban dakarun da suka karbe mulkin kasar Gabon ya bayyana cewa sakon da shugaba Bango ya aiko a makon jiya ya tabbatar da cewa shugaban bai da isasshiyar lafiyar cigaba da yin mulki.

A cikin makon da ya gabata ne dama shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya aiko sojoji na musamman zuwa kasar Gabon domin su kare mutanen kasar sa ko da rikici zai barke a cikin kasar ta Gabon mai dinbin arzikin man fetur.

An hambarar da Gwamnatin gidan shugaba Ali Bongo ne bayan kusan shekaru 50 su na mulkin kasar ta Gabon

Ali Bongo ya hau mulki ne a 2009 bayan Mahaifin sa Omar Bango ya mulki kasar na tsawon shekaru.

#Rariya

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: