Labarai

Da Dumi-Duminsa – An Yi Garkuwa Ga Wasu ‘Yan Kasar Jamus A Jihar Kaduna

An samu rahotanne daga rundunar ‘yan sandan Nijeriya sun tabbatar rahoton yin garkuwa da wasu yan kasar Jamus 2 a jihar Kaduna. Aliyu Usman, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ya bada karin haske game da lamarin inda ya ke cewa mutanen kauye ne sauka shaida wa jami’an tsaro sace mutanen 2 wadanda suka je aikin kare lafiyarsu. Ana kyautata zaton cewar masu satar mutane dan karbar diyya ne suka kwashe su.