Labarai

DA DUMI-DUMI| Za’a kamo Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa A Dalilin Shirin Tambaya Mabudin Ilimi

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja sun tabbatar cewa, hukumar kare hakkin mai mallaka ta kasa (Nigerian Copyright Commision) bisa umurnin ministan yada labarai na kasa ta turawa Sheikh Daurawa da takarda cewa lallai ya kawo kansa gaban hukumar kare hakkin mai mallaka ta kasa a ranar Laraba domin ya bada bayanai da bakin sa ko kuma a umurci kwamishinan ‘yan sanda ya kamo shi.

A jiya Talata ne Sheikh Daurawa ya tura da lauyoyin sa ofishin hukumar kare hakkin mai mallaka (Copyright Commission) domin su yi bayanai game da shirin Tambaya mabudin ilimi. A baynin lauyiyin Sheikh Daurawa sun ce a shirue suke zasu zauna lafiya da gwamnatin tarayya.

Sheikh Daurawa dai ya aike da sako zuwa ga hukumar (Copyright Commission) cewa shirin Tambaya mabudin ilimi shirin sa ne ilimin sa ne ba tare da ya kawo wasu takardu da suke nuna shaidar cewa shirin Tambaya mabudin ilimi mallakin sa ne ba.

Bayan da lauyoyin hukumar (Copyright Commission) suka tura da bayanan da Sheikh Aminu Daurawa ya aiko dashi ga shugaban hukumar kare hakkin mai mallaka ta kasa, nan take shugaban hukumar yace bayanan Sheikh Daurawa basu gamsar da su ba saboda bai kawo takarda ko daya ba, inda ya bada umirni a sake turawa Daurawa sabuwar takarda bisa umurnin ministan yada labarai cewa lallai Daurawa ya kawo kansa a ranar Laraba ko kuma su bada umurnin kwamishinan ‘yan sanda ya kawo masu shi.

-Hausa7 Nig

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: