Da Dumi Dumi: Kwankwaso Zai Tura Yaran Talakawa Karatu Zuwa Kasashen Waje


0 222

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Tsohon gwamnan jahar Kano, kuma jagoran darikar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kammala shirin tura matasa masu sha’awar karo karatu zuwa kasashen waje domin cimma burinsu.

Majiyarmu ta ruwaito hadimar Kwankwaso, Hajiya Binta Sipikin ce ta sanar da haka a shafinta na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda tace gidauniyar Kwankwasiyya na gayyatar matasa masu son cigaba da karatu dasu garzayo domin samun tallafi kyauta.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Sanarwar ta kara da cewa gidauniyar Kwankwasiyya ta bada wannan dama ne ga kowanne fannin ilimi, sai dai tana bukatar matasan da basu haura shekaru 30 bane kawai, kuma suke da digiri mai daraja ta farko, watau First Class.

Gidauniyar na kira ga wadanda suka cika wannan sharadi dasu aika takardar neman gurbin karatun da takardunsu zuwa ga babban daraktan gidauniyar Kwankwasiyya dake gidan Kwankwasiyya, titin Lugarda, cikin unguwar Nassarawa Kano.

Ana bukatar duk masu neman wannan dama dasu mika duk abubuwan da ake bukata cikin kwanaki goma sha hudu, daga cikin takardun da zasu mika akwai shaidar kammala digiri, takardar haihuwa, da dai sauransu

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.