Labarai

Da Dumi Dumi: An Kama Matashin Da Ya Kashe Mahaifiyarsa A Kano

A jiya 4 ga Mayu, 2023 da misalin karfe 10 na dare, an kama Ibrahim Musa, mai shekaru 22 a wani maboyar masu laifi a karamar hukumar Dawakin Tofa, jihar Kano bayan ya daba wa mahaifiyarsa mai shekaru 50 wuka wadda ta mutu har lahira a Rimin Kebbe Quarters, Nassarawa LGA, Kano State.

Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa, sannan kuma ya amsa laifinsa na shan miyagun kwayoyi. Za a gurfanar da shi gaban kotu bayan kammala bincike. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano, CP Mohammed Usaini Gumel, FIPMA, psc ya yaba wa wadanda suka taimaka da bayanan da suka kai ga kama shi, ya kuma yaba wa rundunar ‘yan sandan da suka tabbatar da an kama mai laifin.

Kakakin Rundunar’Yan Sanda Na Jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.