Labarai

DA DUMI-DUMI: An Garzaya Da El-rufa’i Kasar Waje Neman Lafiya

Rahoton Muryar ‘Yanci
Ruhotannin da suke shigo mana daga majiyar mu ta fadar gwamnatin Jihar Kaduna ya tabbatar mana da cewa Mai girma gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir Ahmed El Rufa’i na kwance a wani asibitin ketare ana duba lafiyarsa .

Majiyar mu daya bukaci a sakaya sunansa yace ko a shekaranjiya laraba da shugaban dakarun sojin kasan Najeriya General Yahaya Bello yazo Kaduna ziyarar aiki na musamman akan sha’anin tsaro amma bai samu damar ganawa da gwamnan ba, sai dai yayi wa mataimakiyar gwamna Hajiya Hadiza Balarabe wanda a yanzu ita ke jan ragamar Jihar Kaduna kamin El Rufa’i ya dawo, inda shugaban dakarun sojin yai mata bayanin zuwansa Kaduna.

Duk da dai majiyar mu bai San wani irin ciwo bane yasa aka kai gwamnan asibitin ketare,Amma wakilin mu ya tuntubi Mai taimakawa gwamnan akan sha’anin watsa labarai, Mallam Ibrahim Amma haryanzu da muke rubuta wannan rahoton bai kira yayi mana karin haske ba Kuma bai aiko mana Koda amsar sakon karta kwana da muka tura mai ba.

Zamu kawo maku cikakken rahoton yadda lamarin yake da zarar mun samu sahihin Bayani daga makusanta gwamnan.

Allah ya bashi lafiya da dukkan marasa lafiya dake gida da asibiti Amin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: