Labarai

Da Ɗumi Ɗuminsu: Rundunar Ƴan Sandan Jihar Katsina Ta Yi Sabon Jami’in Huɗɗa Da Jama’a (PPRO)

Da Ɗumi Ɗuminsu: Rundunar Ƴan Sandan Jihar Katsina Ta Yi Sabon Jami’in Huɗɗa Da Jama’a (PPRO)

 

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta naɗa sabon jami’in huɗɗa da jama’a (PPRO) ASP Abubakar Sadiq Aliyu, jami’in Ɗan sandan dai ya karɓi ragamar aiki ne daga babban Sufeton ƴan sanda CSP Isah Gambo .

 

A cewar wata sanarwa da tsohun jami’in Huɗɗa da jama’a na rundunar ya fitar tace, naɗin sabon PPRO ɗin ya biyo bayan samun girma da tsohun jami’in huɗɗa da Jama’ar ya samu na Muƙamin shugaban ofishin huɗɗa da jama’a na shiyya 14 dake nan Katsina wato Offishin AIG zone 14

 

A baya dai ASP Abubakar Sadiq Aliyu shi ne tsohon mataimakin jami’in huɗɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar.

 

ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya kammala karatunsa ne a babbar makarantar horar da Jami’an ƴan sandan Najeriya da ke Wudil a jihar Kano, Sadiq haifafen jihar Kaduna ne.

About the author

habibjs

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.