Siyasa

Da ɗumi-ɗumi: Gwamnan Zamfara ya sauya sheƙa zuwa APC

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Gwamnan ya shaida wa wakiliyar Freedom Radio Jamila Ado Mai Wuƙa cewa, ya fice daga jam’iyyar, amma bai yi ƙarin bayani kan dalilan hakan ba.

A cewar sa, a ranar Talata mai zuwa ne za a yi bikin karɓar sa zuwa APC.

Tuni dai magoya bayan jam’iyyar suka shiga yin maraba da Gwamnan, musamman a kafafen sada zumunta.

Daga ciki har da hadimin shugaban ƙasa Malam Bashir Ahmad.

A nasu ɓangaren magoya bayan jam’iyyar PDP tuni suka shiga bayyana takaicinsu a kai.

A wani saƙo da ya wallafa, mai taimakawa tsohon Gwamnan Kano Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso kan kafafen sada zumunta Saifullahi Hassan, ya bayyana damuwa.

Yana mai cewa, ba haka suka so ba, inda ya nemi magoya bayan PDP na jihar Zamfara da su yi haƙuri.

Sedai kuma labari ya sosawa mutane da dama rai yayinda suka ringa comment akan lamarin kamar haka.

 

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement