Da ɗumi-ɗumi | Ƴan kidinafin sun sako ‘ƴan Kasuwar Kwari sama da 20 da suka sace

0 0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

‘Ƴan kidinafin sun sako’ ƴan kasuwar Kwari sama da 20 da suka sace a hanyar zuwa kasuwar Aba ta jihar Abia.

Jami’in yaɗa labaran kasuwar, Alhaji Mansur Haruna Ɗandago ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

‘Ƴan kasuwar sun kwashe kwanaki biyar a hannun masu garkuwa da mutanen kafin a yanzu da suka sako su.

Alhaji Mansur ya ce, an sako su ne bayan da aka biya kuɗin fansa sai dai bai bayyana adadin kuɗin da aka biya ba.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 783

Yanzu haka dai tuni ana sa ran isowarsu Kano kamar yadda ya shaida mana.

Ku nemi jaridar Almizan ranar Juma’a mai zuwa don jin cikakken labarin yadda wannan mummunan al’amari ya kasance.

Hoton kasuwar Kwari Kano

#Kanomedia

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: