Labarai

Cutar Kwalara Ta Kashe Mutum 60 A Abuja

Daga Mahdi M. Muhammad,
Cutar kwalara ta ci rayukan mutane akalla 60 a babban birnin tarayya Abuja.

Cutar kwalara ta fara barke ​​ne a cikin Majalisar karamar hukumar Abuja a ranar 23 ga Yunin 2021, inda ta kashe akalla bakwai daga cikin 91 da ake zargi sun kamu.

Karamar Ministar Abuja, Dakta Ramatu Tijjani Aliyu, ta tabbatar da adadin mutanen da suka mutu a ci gaba da wayar da kan al’umma kan cutar kwalara da sauran munanan cututtukan gudawa da suka barke a yankunan Pyakasa da Gwagwa da ke babban birnin kasar.

Ta kuma bayyana cewa, wadanda ake zargin sun tashi daga 604 zuwa 698 cikin awanni 72.

A cewar mai taimaka wa Ministar kan harkokin yada labarai, Austin Elemue, Ramatu ta samu wakilcin Babban Sakatare na hukumar kula da lafiya a matakin farko ta FCT, Dakta Iwot Ndaeyo.

Ta kara da cewa, karamar hukumar Abaji ta samu mutane uku da ake zargin sun kamu, ba mutuwa ko daya, karamar hukumar Abuja Municipal (AMAC) ta rubuta 281 da ake zargin sun kamu da cutar tare da mutuwar mutane 22, yayin da aaramar hukumar Bwari ta samu rahoton 134 da ake zargin sun kamu da cutar tare da mutuwar 22.

Har ila yau, majalisar Gwagwalada ta dauki mutane 220 da ake zargin sun kamu da cutar tare da mutuwar mutane tara, Kuje yana da mutane 23 da ake zargin sun kamu da cutar tare da mace-mace hudu kuma Kwali ya kai mutum 37 da ake zargin sun kamu tare da mutuwar mutane uku.

Ministar, wacce ta ce, ba a yarda da wannan mummunan lamarin ba, ta ba da tabbacin cewa, gwamnatin ba za ta dunkule hannu ta na kallon mazauna yankin suna mutuwa ba tare da wani taimako ba game da cututtukan da za a iya kiyayewa.

“Dole ne mu dauki dukkan matakan da suka dace don dakile yaduwar cutar,” in ji ta, tare da yin kira ga mazauna da masu ruwa da tsaki da su yada sakon rigakafin cutar kwalara, tsabtace muhalli tare da tsabtace hannu a cikin al’ummominsu.

Haka zalika, Shugaban karamar Hukumar Municipal na Abuja (AMAC), Honarabul Abdullahi Adamu Candido, ya sake nanata kudirin majalisarsa na dakile yaduwar cutar a tsakanin al’umma.

Ya kara da cewa, sashin kula da lafiya a matakin farko na karamar hukumar ta fara rangadin fadakarwa zuwa dukkanin manyan masarautun guda hudu a AMAC domin fadakar da sarakunan gargajiya da talakawansu game da barkewar cutar kwalara da kuma hanyoyin kariya.

“A bangaren mu na karamar hukumar, mun shiga cikin aiki nan take muka sami labarin barkewar da kuma tabbatar da ita a watan Yuni. Mun hanzarta tattara jami’an mu na kiwon lafiya a duk cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko domin amsar gaugawa. Bayan shawarwari daga rahoton bullar cutar, mun samar da kudade don sayen magunguna cikin sauri, jiko da sauran kayan magani da kayan masarufi ban da wadanda muka karba daga Sashen Kiwon Lafiyar Jama’a na FCT,” in ji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: