Wasanni

Cristiano Ronaldo ya gurfana a gaban kuliya kan haraji

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya bayyana a gaban kuliya nan gaba a birnin Madrid domin ya bayar da bahasi kan tuhumar sa da ake yi da zamba cikin aminci wajen biyan haraji.

Masu shigara da kara dai na zargin Ronaldo, wanda shi ne mai rike kanbun gwarzon dan kwallon duniya, da kin biyan harajin da ya kai dala miliyan 17.

Sai dai kuma dan kwallon ya yi watsi da wannan zargi.

 

Idan dai har aka samu dan wasan dan asalin kasar Portugal da laifi kan abin da ake tuhumarsa da shi to zai iya fuskantar zaman gidan kaso.

Ronaldo, mai shekara 32, shi ne na baya-bayan nan a jerin ‘yan wasan da hukumomi a Spaniya ke tuhuma kan batun haraji.

A kwanakin baya ma wata kotu ta samu dan kwallon Barcelona Lionel Messi da laifin kin biyan haraji, inda aka yanke masa hkuncin daurin shekara biyu.

Sai dai an mayar da hukuncin tara kamar yadda wani shashi na dokar kasar Spaniya ya tanada.

‘Yan wasa da dama dai na fuskantar tuhumar kin biyan haraji a kasar ta Spaniya, abin da wasu ke dangantawa da rashin kyawun tsarin tattara haraji na kasar.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.