Wasanni

Coutinho: Liverpool ta kara watsi da tayin Barcelona

A kakar da ta wuce Philippe Coutinho ya zura kwallo 14 a raga

Liverpool ta kara yin watsi da tayin fam miliyan 90 da Barcelona ta yi wa gwanin dan wasanta na Brazil Philippe Coutinho.

Nan take ba wata-wata Liverpool ta yi watsi da tayin na biyu kan dan wasan na Brazil mai shekara 25, hatta karin fam miliyan 13 da rabi da kungiyar ta Spaniya ta yi a kai bai sa jami’an na Liverpool sun karyo ba.

Sai ma kara jaddada matsayinsu suka yi na cewa Coutinhon wanda suka sayo daga Inter Milan a kan fam miliyan 8 da rabi a 2013, ba fa na sayarwa ba ne.

 

A makon da ya wuce ne Barcelona ta sayar da Neymar na Brazil ga zakarun Faransa, Paris St-Germain a kan kudin da ba a taba sayen wani dan tamaula ba a duniya, har fam miliyan 200.

A watan Janairu ne Coutinho, wanda a kakar da ta wuce ya ci kwallo 14, kuma ya tafi jinyar mako shida ta ciwon idon kafa, ya sake kulla kwantiragin shekara biyar da Liverpool, yarjejeniyar da ba ta kunshi wata sidira ko dama ta sayar da shi ba.

Daman tun a watan Yuli da Barcelona ta fara taya dan wasan fam miliyan 72, kociyan Liverpool Jurgen Klopp ya ce kungiyar ba mai sayar da ‘yan wasa ba ce, kuma tun a lokacin su a wurinsu maganar ta kare kenan.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.