Wasanni

Copa America: Neymar Da Messi Za Su Gwabza A Wasan Karshe

Tawagar kasar Argentina za ta fafata wasan karshe tsakaninta da tawagar kasar Brazil bayan da tawagar wadda Messi yake jagoranta ta doke kasar Chile a safiyar ranar Laraba a wasan kusa dana karshen da suka fafata.

A ranar Talata ne dan kwallon Brazil, Neymar, ya ce burinsa shi ne kasarsa ta buga wasan karshe na cin kofin kasashen Amurka watau Copa America da Argentina domin ya gwada karfin tawagar tasu.

Brazil ta kai wasan karshe na gasar da take daukar bakunci bayan ta samu galaba a kan Peru da ci daya mai ban haushi kuma dan wasan PSG din ya haskaka a wasan da suka fafata da Peru inda ya bai wa Lucas Pakuetakwallon da ya zura a ragar Peru.

Sai a ranar Lahadi za a buga wasan karshe na gasar tsakanin Brazil da kasar da ta samu galaba tsakanin Argentina da Colombia kuma ana ganin wannan shine wasan kofin karshe da Messi zai wakilci Argentina a yankin kudancin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: