Kannywood

Ciwona Bana Tashi Bane, Ahmad Aliyu Tage Yasanar Da Iyalinsa

JARUMIN barkwanci kuma daɗaɗɗen mai ɗaukar hoton bidiyo (cameraman) a Kannywood, Malam Ahmad Aliyu Tage, ya faɗa wa iyalan sa a jiya cewa ciwon sa ba na tashi ba ne, kuma ya ce don Allah idan ya mutu to a yafe masa.

Ɗan yayan sa, Umar Muhammad Aliyu, shi ne ya faɗa wa mujallar Fim haka jim kaɗan bayan an rufe gawar marigayin a maƙabartar Tarauni, Kano.

Tage ya rasu ne a yau a asibiti a Kano bayan ya yu jinyar ciwon bugun zuciya da ya samu.

Ya mutu ya na da kimanin shekara 55 a duniya, kuma ya bar ‘ya’ya 21 da matan sa na aure guda biyu.

Ɗimbin mutane, ciki har da abokan sana’ar sa ‘yan fim, sun halarci sallar jana’izar sa wadda aka gudanar a gidan sa da ke unguwar Sheka Ƙarshen Kwalta da ƙarfe 3:55 na yamma.

Daga nan aka ɗunguma aka raka shi zuwa makwancin sa a maƙabartar Tarauni.

Jim kaɗan bayan kammala binne gawar ne mujallar Fim ta so jin ta bakin ɗaya daga cikin ‘ya’yan marigayin, to sai dai hakan ba ta samu ba saboda yanayin da ya ke ciki na alhini.

A nan ne ɗan wan Tagen mai suna Umar ya bayyana mana kaɗuwar su dangane da wannan mutuwa da ya kwatanta da rashi ne ba ma ga su iyalan sa kaɗai ba har ma ga duniya baki ɗaya.
Umar ya ce, “Ƙanin baban mu mutumin kirki ne domin ba shi da abokan faɗa kuma mutum ne mai sada zumunci. Kullum tsakanin sa da al’umma sai haba-haba. A duk lokacin da ka je gun sa ba shi da aiki sai faɗin me ka ke buƙata, abinci ka ke so ko ruwa da sauran su.

“Ba abin da zamu ce sai godiya domin kuwa ɗabi’un sa na kirki ne.

“Kullum kiran sa shi ne a sada zumunci, shi ne burin sa kullum.

“Ni kamar ɗa na ke a gun sa, amma ya maida ni kamar aboki saboda ko da yaushe mu na tare da shi. Yau tsawon kwana uku kenan mu na tare da shi.”

Umar ya ce a jiya marigayin ya sanar da shi cewa ba zai tashi daga wannan ciwon ba.

Ya ce, “Jiya mu na tare da shi, ya ke sanar da ni cewa wannan cutar ba ta tashi ba ce, ya ke cewa in ya mutu a yafe masa. Kuma wannan shi ne ƙarshen magana ta da shi.”

‘Yan fim waɗanda mujallar Fim ta gani a wurin jana’izar sun haɗa da Ayatullahi Tage, Mustapha Nabraska, Alhassan Kwalle, Shu’aibu Idris Lilisco, Lawan Ahmad, Hassan Giggs, Lawan Garba Taura, Daddy Hikima, Shehu Hassan Kano, Mustapha Musty, Baba Ari, Tijjani Faraga, Sunusi Oscar442, Abba Al-Mustapha, Aminu Ladan (Alan Waƙa), Ali Rabi’u Ali (Daddy), Shu’aibu Yawale, Auwalu Isma’il Marshal, da Bala Anas Babinlata.

Mu na addu’ar Allah ya jiƙan Ahmad Tage, ya yi masa rahama, amin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: